An yanke wa maharin New York hukuncin daurin rai-da-rai

Ahmad Khan Rahimi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rahimi a lokacin shari'ar da aka yi masa a watan Mayun 2017

Mutumin da ya tada wasu bama-bamai a birnin New York da New Jersey a 2016 zai shafe sauran rayuwarsa a kurkuku.

Raimi ya raunata mutum 30 bayan da ya kai hari da wani bam.

Dan asalin Afghanistan din wanda amma dan Amurka ne ya shiga hannun jami'an tsaro ne bayan musayar wuta, ya sanar da kotu cewa "ba ya kin jinin kowa".

Masu shigar da kara sun ce mutumin mai shekara 30 da haihuwa bai nuna nadamar aika-aikar da ya yi ba kuma ya na kokarin shigar da wasu fursunoni kungiyar IS.

An sami Raimi, wanda aka lakaba wa sunan "Chelsea bomber' da dukkan lafuka takwas din da masu shigar da kara suka gabatar a kotu.

Gwamnan jihar New York Andrew Cuomo ya bayyana cewa "an yi adalci".

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hotunan tashar talabijin ta WABC sun nuna lokacin da ya shiga hannu da raunuka a jikinsa

Mahaifin Raimi ne ya kai kararsa a wajen hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, wato FBI, inda ya kira shi dan ta'adda a wata hira da yayi da tashar talabijin ta NBC.

Daurin da aka yi masa na tabbatar da cewa zai yi wuya a sake shi kafin shekarunsa a duniya su kare.