Israel: 'Yan sanda na son Netanyahu ya gurfana a kotu

Binyamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images

Jami'an 'yan sandan Isra'ila sun mika wa masu shigar da kara bayanai da ke cewa a gurfanar da firai minista Binyamin Netanyahu a gaban shari'a saboda tuhumar cin hanci da rashawa, da zamba cikin aminci.

'Yan sandan sun nemi a gurfanar da firai ministan akan batutuwa biyu.

Na farko ya shafi wata maganar karban kyautuka da ya yi domin yi wa wadanda suka ba shi kyautar wani aiki.

Yan sandan sun ce Binyamin Netanyahu ya rika ba wasu abokansa ayyuka na musamman bayan ya karbi kaya masu matukar darja da tsada kamar giyar champagne da tabar siga da gwalagwalai.

Na biyu shi ne batun katsalandan da ya ke yi wa kafafen watsa labarai.

Jami'an tsaro sun ce Mista Netanyahu ya nemi wata jarida ta fifita shi inda shi kuma ya yi alkawarin dakile wasu jaridu kishiyoyinta.

Amma shugaban na Isra'ila ya yi watsi da matakin na 'yan sanda: "A shekarun baya an rika neman gurfanar da ni fiye da sau 15 domin a sauke ni daga mukamina. Dukkansu sun fara ne da labarai a jarida da talabijin masu cewa na yi manyan laifuka."

Ya kara da ce, "Wasu ma har da manyan tuhume-tuhume daga 'yan sanda kamar wannan. Amma dukkan wadannan yunkurin ba su yi min komai ba. Saboda na san gaskiya, kuma ina fada muku, a wannan karon ma, babu abin da zai faru."

Jam'iyyun adawa sun yi kira ga Mista Netanyahu da ya sauka daga mukaminsa.

Amma a halin yanzu babu wanda ya fi shi tasiri a siyasar kasar.

Za a mika bukatar 'yan sandan ga lauyan gwamnati Avichai Mandelblit.

Ya kuma rage gare shi da ya yanke hukunci game da gurfanar da firai ministan ko kuma ya yi watsi da bukatar baki daya.