South Africa: 'Yan sanda sun kai samame gidan iyalan Gupta

Members of the Hawks special police unit stand guard outside Gupta home Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana can a na binciken gidan iyalan na Gupta da ke birnin Johannesburg

'Yan sanda sun damke mutum biyu a wani samame a gidan iyalan attajiri Gupta na Afirka ta Kudu a wani bincike da gwamnati ke yi.

Attajirai Gupta, wanda haifaffun kasar Indiya ne na fuskantar tuhuma ta "makare hukumar kasar" ta hanyar amfani da dangantakarsu da shugaba Jacob Zuma domin samun manyan kwangiloli daga gwamnati.

Iyalan Guptan da Mista Zuma sun musanta wadannan tuhume-tuhumen da ake musu.

Mr Zuma is under pressure to resign, in part because of links to the Guptas.

Shi kuma shugaba Zuma na fuskantar matsin lamba na ya sauka daga mukaminsa saboda dangantakarsa da iyalan Guptan.

Hakkin mallakar hoto AFP

Labarai masu alaka