An yanke hukuncin daurin shekara 60 kan kwamandan Boko Haram

sojoji Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata babbar kotun Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara 60 kan wani dan kungiyar Boko Haram.

Mutumin, mai suna Abba Umar, mai shekara 22, wanda kuma kwamanda kungiyar ne ya ce bai yi nadamar zaman dan kungiyar Boko Haram ba.

Kotun da ke zamanta a Kainji na jihar Niger da ke arewacin Najeriya ta ce Abba ya amince cewa shi dan Boko Haram ne ya rantse cewa ko yanzu aka sake shi zai koma dajin Sambisa domin ya ci gaba da kai hare-hare.

An same shi da laifin kai hare-hare a yankuna da dama.

Wata sanarwa da Salihu Othman Isah, mai magana da yawun ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya aike wa maneman labarai ta ce an yanke wa Abba Umar hukuncin ne saboda samun sa da hannu a aikata laifuka biyar.

Hukunci da laifukan su ne:

Daya: Daurin shekara 15 saboda ya amince da kasancewa dan Boko Haram

Biyu: Daurin shekara 30 saboda yunkurin kai harin bam a makarantar sakandare ta Govt. Day Pilot, Gombe.

Uku: Daurin shekara 60 a gidan yari saboda aikatalaifin ta'addanci inda aka kama shi da makamai.

Hudu: Daurin shekara 15 a kurkuku saboda samun horon aikata ta'addanci a Dajin Sambisa

Biyar: Daurin shekara bakwai saboda kin bayar da bayanai kan shugabannin kungiyar Boko Haram.

Sanarwar ta karada cewa Abba Umar ya amince da aikata dukkan laifukan biyar.

Hakkin mallakar hoto AFP/BOKO HARAM

Labarai masu alaka