Mun ceto mutum 3,475 daga BH a shekara guda – Sojoji

Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY
Image caption Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kubutar da farar hulla 3,475 daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram a cikin shekara guda.

Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da kungiyar Boko Haram Manjo Janar Nicolas Rogers shi ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai a birnin Maiduguri na jihar Borno.

An dai watsa taron manema labarai kai tsaye ta gidan talabijin na kasar a kokarin da sojojin suka ce suna yi na fadakar da al'umma ayyukan su a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Manjo Rogers ya kuma bayyana cewa dakarun sojin kasar sun hallaka mayakan Boko Haram 167 a artabu dabam daban da suka yi tare da kuma cafke 'yan kungiyar 167 a shekara guda.

Rundunar ta kara da cewa, a halin yanzu mayakan Boko Haram sun tagayyara bayan sojojin kasar sun karya lagon su a dajin Sambisa.

Haka kuma ''jiragen yakin sojojin sama sun yi ta kai hare-hare ta sama a sansanonin Boko Haram inda suka hana mayakan sakat''- in ji kwamandan sojojin.

Kwamandan rundunar ya kuma ce akwai wasu sojojin kasar da suka rasa ransu a fafatawa da 'yan Boko Haram, koda yake bai bayyana adadin sojojin da suka rasu ba.

Ya kuma mika ta'aziyya ga iyalan sojojin da suka rasu inda ya ce dakarun sojin sun lashi takobin kawar da masu ayyukan ta'addanci a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Labarai masu alaka