Kullum ranar soyayya ce a addinin Musulunci – Sheikh Daurawa

Val Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wadansu daliban Jami'ar Punjab na kasar Pakistan yayin da suke zanga-zangar adawa da ranar Valentine

Bahaushe mutum ne mai tsananin rikon al`adunsa, kuma galibin Hausawa Musulmi ne, wadanda kunya da koyarwar addinin ke taka muhimmiyar rawa a harkokinsa na rayuwa.

A ranar Laraba ne ake bikin ranar masoya ta duniya; shin yaya Hausawa ke kallon wannan rana?

'Yan magana dai kan ce soyayya kogi ne, kuma idan ba ka sha to ka ratsa.

Don haka kamar sauran bil`adama, Hausawa masoya kan nuna zunzurutun kauna ga junansu, amma saboda al`adar kunya ba kasafai suke nuna soyayyar a fili ba.

Hatta a ranar masoya irin ta yau, kuma birni irin Kano mai miliyoyin Hausawa, a ziyarar da na kai wuraren da jama`a kan taru, wadanda na gani suna magagin soyayya kalilan ne.

Ganin yadda Hausawa ke dogaro ga addini wajen kaurace wa ranar Valantine, wakilin BBC a Kano Ibrahim Isa tuntubi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, babban Malamin addinin Musulunci kan ko da wani lokaci da Musulmi kan yi bikin soyayya?

  • Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da shi:
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Sheikh Aminu Daurawa

Labarai masu alaka