Wane ne Shugaba Jacob Zuma?

South African President and African National Congress (ANC) President Jacob Zuma leads hundreds of supporters in singing a song during a campaign event at the Inter-fellowship Church in Wentworth township, outside of Durban, on April 9, 2014 Hakkin mallakar hoto AFP

Jacob Zuma shi ne shugaban Afrika ta Kudu da ya fi janyo cece kuce tun bayan da aka kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekarar 1994.

Dan siyasa ne daya sha tsallake rijiya da baya, wanda ba kowane mutum bane zai iya tsallake siradin daya shiga.

Sai dai Mr Zuma, wanda iyayensa talakawa ne da yayi gudun hijira don yaki da wariyar launin fata, ya sha gwagwarmaya kafin ya kaiga matsayin "shugaban Jama'a".

Ba shi ne shugaban jam'iyyar ANC mai mulki ba, kuma duk da cewa ya sha musanta zargin cin hanci da rashawa da ake masa, a karshe dai wannan ne ya janyo karshen sa.

karo na 9 kenan da aka kada masa kuri'ar yankan kauna a Majalisar dokokin kafin ya bar mulki.

A shekarun baya dai, ba mai yiwuwa bane a yi watsi da tasirin Mr Zuma:

Sunan da ake kiran sa ta kabilar Zulu, Gedleyihlekisa, wanda ke nufin mutumin da ke yiwa makiyarsa dariyar mugunta.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cyril Ramaphosa (a hagu) shi ne ya maye gurbin Mr Zuma a shugabancin ANC

Sai da aka yi ta gwagwarmaya da shi kafin ya tafi, duk da cewa an jima wasu alamu sun nuna cewa karshensa ya zo kusa.

Koda yake tun kafin ya zama shugaban kasa, lauyoyin sa sun sha kwaramniya akan sa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Zuma ya shahara wajen taka rawa.

An jima ana kallon cewa shugabancin Mr Zuma ya kawo karshe tun ma kafin cikar wa'adin sa.

Kafin zaben shekarar 2009, ya sha fama da zargin aikata fyade da kuma cin hanci da rashawa.

Daga bisani an wanke shi daga zargin aikata fyade ga wata abokiyar sa mai dauke da kwayar cutar HIV a shekarar 2006 - koda yake, bayanan da ya yiwa kotu cewa ya kauce ne don gudun kada ya kamu da HIV zai jima yana damunsa har karshen mulkin sa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Jacob Zuma

Sai dai zargin cin hanci da rasha da ake ta yi masa ya kasa kaucewa duk kuwa da cewa wata hukumar shari'a ta kasar ta janye tuhumar, makonni kafin a kada kuri'a wanda ya bashi damar lashe zabe.

Sai dai kuma ba'a manta ba da tuhuma kan halatta kudaden haram wanda ya fito fili bayan cinikin makamai na dala biliyan 5 da aka sa hannu a shekarar 1999 wanda kuma ake ta cece kuce akai.

A shekarar 2017 ne kuma kotun kolin kasar ta yanke hukunci cewa a dawo a binciki tuhume-tuhume 18 kan zargin aikata cin hanci da rashawa da ake masa.

Koda yake ya sha musanta tuhume-tuhumen inda ya ce zai yi murabus idan har aka tabbatar cewa ya aikata ba dai-dai ba.

'"Shugabana Jama'a"'

Kwarjinin sa ne yasa ya lashe zabe a shekarar 2009, kuma magoya bayan sa sun rika nuna banbamcin sa da shugaba Thabo Mbeki, wanda aka rika kallo a matsayin shugaba da baya haba-haba da jama'a.

"Mutum ne mai jin magana baya nuna kansa a matsayin shi shugaba ne da yafi kowa sani,"- inji daya daga cikin magoya bayan sa da yake bambanta shi da Mr Mbeki.

An dai zargi abokan Mr Mbeki ne kulla makarkashiyar tuhumar Mr Zuma bayan ya kwace shugabancin ANC a shekarar 2007.

Ana ganin irin tarbiyar da Mr Zuma ya samu da kuma karfafa tsarin gargajiya sun taimaka wajen kara masa farin jini tsakanin talakawan Afrika ta Kudu da dama musamman a yankunan karkara.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gidan Mr Zuma a Nkandla ya janyo masa fitini a fagen siyasa

Zuma mai shekaru 75 yana alfahari da kasancewar sa mutum mai mata fiye da daya, inda yake bin tsarin kabilar sa ta Zulu- kuma yanzu haka matan sa hudu.

Ya yi aure har sau shida kuma yana da yara 21.

Daya daga cikin matan sa 'yar kasar Mozambique Kate Mantsho, ta kashe kanta a shekarar 2000.

Sai dai kuma an san halayyarsa ta neman mata a waje har ma ya taba yiwa wata ciki ta haifa masa da.

Kuma ba'a jima ba ne mutane suka nuna shakku akan ko ya dace a rika kallon sa a matsayin "shugaban Jama'a".

Daga shekarar 2013 kimar sa ta ragu matuka bayan ya yi amfani da kudaden gwamnati wajen kawata gidan sa a kauyen Nkandla, da ke arewacin KwaZulu-Natal.

A lokacin jana'izar shugaban Afrika ta Kudu bakar fata na farko Nelson Mandela, a watan disambar shekarar, magoya bayan ANC sun rika yi masa ehu.

Lamarin dai ya faru ne a gaban manyan baki daga wasu kasashe da suka halarci jana'izar cikin su har da tsohon shugaban Amurka Barack Obama.

"Ya na cin abinci yayin da mu muke zaune cikin yunwa,"- inji daya daga cikin masu yi masa ehu.

Wannan ya nuna irin yadda mutane suka harzuka saboda amfani da kudaden gwamnati wajen kawata gidan sa a kauyen Nkandla ya koma gidan alfarma.

Tuni Mr Zuma ya biya kudaden da aka kashe wajen kawata gidan.


Gwagwarmayar da Zuma ya sha ta fuskar shari'a:

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Jacob Zuma
  • 2005: An tuhume shi da cin hanci da rashawa a cinikin makamai daya kai biliyoyin daloli a shekarar 1999- koda yake an janye tuhumar kafin ya zama shugaban kasa a 2009
  • 2016: Kotu ta bada umurni a a binciki tuhume-tuhume 18 kan zargin aikata cin hanci da rashawa da ake masa kuma daukaka kara.
  • 2005: An tuhume shi da yiwa wata abokiyar sa fyade- an wanke shi a a kan tuhumar a 2006
  • 2016: Kotu ta zartar da hukunci cewa ya saba rantsuwar aiki na amfani kudaden gwamnati wajen gyara gidansa a Nkandla - ya biya kudaden
  • 2017: Mai shigar da kara na gwamnati ya bukaci ya nada alkalai da zasu binciki zargin alaka da iyalan gidan attajirin nanGupta - Ya musanta zarge zargen har da suma iyalan Guptas
  • 2018: Zuma ya amince da bincike

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba