Jagoran 'yan adawan Zimbabwe Morgan Tsvangirai ya rasu

Morgan Tsvangirai speaks to supporters at a rally in Harare in October 2008 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Marigayin ya rika kalubalantar Shugaba Mugabe yayin da ya kwashe lokaci mai tsawo yana mulkin kasar

Jagoran 'yan adawan Zimbabwe Morgan Tsvangirai ya rasu, kamar yadda wani babban jami'i a jam'iyyar MDC ya bayyana.

Mista Tsvangirai wanda ya rasu yana da shekara 65, ya taba zama firaministan kasar.

Marigayin wanda ya rasu da yammacin ranar Laraba, ya yi fama ne da ciwon kansar uwar hanji, kamar yadda mataimakin shugaban jam'iyyar MDC Elias Mudzuri ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Jagoran 'yan hamayyan ya shafe shekaru masu yawa yana adawa da tsohon Shugaban Kasar Robert Mugabe.

Har ila yau, Mista Tsvangirai ya sha dauri a lokuta daban-daban a karkashin mulkin Shugaba Mugabe.

A shekarar 2000 ne marigayin ya kafa jam'iyyar MDC, inda ya rika kalubalantar Shugaba Mugabe yayin da ya kwashe lokaci mai tsawo yana mulkin kasar.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka