Tsohon Dalibi ya bude wuta a makaranta

Wannan shi ne na goma sha tara a jerin harbe-harbe a makarantun Amurka a wannan shekarar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan shi ne na goma sha tara a jerin harbe-harbe a makarantun Amurka a wannan shekarar

A kalla 'yan makaranta goma sha bakwai da manya a ka kashe bayan da wani ya bude wuta a Makarantar sakandire ta Marjory Stoneman Douglas a Parkland Jihar Florida da ke kasar Amurka.

'Yan sanda sun kama wanda a ke zargi da yin harbin, Nikolas Cruz-- wani tsohon dalibin makarantar wanda ya rika nuna tsananin kauna ga bindigogi.

An sallami Nikolas Cruz ne daga makarantar bisa dalilan ladabtarwa kuma ya nuna alamun son ya cutar da dalibai don haka aka haramta masa shiga harabar makarantar.

Ya shiga harabar makarantar ne ya na dauke da bindigogi. Ya kunna kararrawar sanar da tashin gobara sannan ya fitar da dalibai daga cikin ajujuwa sannan ya bude wuta.

Wannan shi ne na goma sha tara a jerin harbe-harbe a makarantun Amurka a wannan shekarar.

Labarai masu alaka