A na zargin Oxfam da cin zarafin mata

Fitacciyar mai fita a fina-finan nan wacce kuma jakadiyar kungiyar ce ta musamman, Minnie Driver ta ajiye aikinta da kungiyar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fitacciyar mai fita a fina-finan nan wacce kuma jakadiyar kungiyar ce ta musamman, Minnie Driver ta ajiye aikinta da kungiyar

Sakamakon badakalar cin zarafin mata da ake zargin kungiyar agaji ta Oxfam da aikatawa a kasashen Haiti da Chadi, yanzu haka fitacciyar mai fita a fina-finan nan wacce kuma jakadiyar kungiyar ce ta musamman, Minnie Driver ta ajiye aikinta da kungiyar.

Jarumar da ta shafe akalla shekara 20 tana nuna goyon bayanta ga irin ayyukan jin-kai da kungiyar ke gudanarwa ta ce abin takaici ne, da kunya a ce ma'aikatan kungiyar na aikata lalata da kananan yara da sunan ba su agaji.

Haka ita ma Kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce ta samu korafe korafen fasikanci akan ma'aikatanta 24 bara.

Kungiyar ta MSF din ta ce an kori ma'aikata 19 a kan wadannan zarge zargen, wasu kuma an basu gargadi ko dakatar da su.