Cyril Ramaphosa ne sabon shugaban South Africa

Cyril Ramaphosa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cyril Ramaphosa ne sabon mukaddashin shugaban kasar Afirka ta Kudu

An nada Cyril Ramaphosa a matsayin mukaddashin shugaban kasar Afirka ta Kudu, bayan da Jacob Zuma ya yi murabus a daren Laraba.

Wani babban jami'in jam'iyyar ANC mai mulkin kasar Jessie Duarte ya yi kira ga 'yan majalisar kasar su ba Mista Cyril Ramaphosa goyon baya a lokacin da za su kada kuri'a akai ranar Alhamis ko Jumma'a.

Attajirin dan kasuwar shi ne ya jagranci jam'iyyar ta ANC tun watan Disamba.

Tun a watan Disamba ne ake matsa wa tsohon shugaba Jacob Zuma lamba domin ya yi murabus, a lokacin da Cyril Ramaphosa ya maye gurbinsa a matsayin shugaban jam'iyyar ANC.

Labarai masu alaka