Ganduje ba zai iya ba mu wajen kiwo ba - Fulani makiyaya

makiyaya Hakkin mallakar hoto Getty Images

Fulani makiyaya a Najeriya sun ce suna tababa a kan wani alwashin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi, cewar jihar Kano za ta samar da wurin kiwo ga Fulanin da ke kasar baki daya.

Wasu makiyaya da ke jihar dai sun ce wurin kiwon da ake da shi bai wadaci shanun cikin jihar ba, ballantana a bude kofa ga makwabta.

A baya-bayan nan ne gwamnatin Kanon ta yi wa Fulanin Najeriya wannan tayin, wanda ake ganin cewa zai taimaka wajen rage rikicin da ake yi da makiyaya a kasar.

Amma duk da haka wasu makiyaya a jihar na cewa suna maraba da tayin da gwamnatin Ganduje ta yi ga 'yan uwansu na samar musu wurin kiwo, matakin da suke cewa zai cire musu dangi daga halin kaka-nika-yin da suka tsinci kansu.

Sai dai da yawa daga cikin Fulanin na kokwanto dangane da faruwar lamarin, idan suka yi la'akari da cewa shanunsu da ke gida ma wata rayuwa suke yi ta hannu-baka-hannu-kwarya, sakamakon zargin da suke na warwason da mahukunta ke yi da ragowar buratali da wuraren kiwon da ke jihar.

Don haka ba su san wane dabo gwamnati za ta yi ba na wadata shanunsu da filin kiwo, kamar yadda Alhaji Ahmed Canji Mangari, shugaban kungiyar cigaban Fulani ta Gan-Allah, reshen jihar Kano ya fada.

Sai dai gwamnatin jihar Kano, kamar yadda kwamishin aikin gona, Alhaji Nasiru Gawuna ke cewa ba wasa a cikin ikirarin rungumar makiyaya da gwamna Ganduje ya yi.

"Idan ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa to ya daka dutse ne, muna wannan aikin ne da hadin gwiwar gwamnatin tarayya. Filinmu na kiwo na Dan Soshiye da ke karamar hukumar Kiru, za a gina asibiti da makaranta, a samar da ruwa saboda dabbobin makiyaya.

"Irin wannan fili muna da 11 a kananan hukumomi daban-daban, kuma tuni har 'yan kwangila sun fara aiki.

"Za a shuka ciyawa wacce za ta dinga tasowa ko yaushe. Muna kuma da dajin Falgore wanda zai iya daukar shanu kusan miliyan biyar."

Gwamnatin Kanon dai ta bayyana cewa bayan gwamnatin tarayya, ta kulla alaka da wasu hukumomi a gida da wajen Najeriya wadanda za su kafa kamfanonin da za su sarrafa nama da sauran kayan amfani daga Saniya, ta yadda za a ci gajiyar filayen kiwon wajen samar da aikin yi ga jama'a.

Dangane da burtalin da makiyaya ke kukan ana cinyewa kuwa, kwamishinan ya ce gwamnati ta yi nisa wajen kwato su, hasalima hidimar kula da filaye ta koma karkashin gwamnan jiha.

Sai dai duk da irin wannan farar-aniya da gwamnatin Kano ke ikirarin kudurtawa, makiyayan sun ce da wuya su samu cikakkiyar gamsuwa, sai sun gani a kasa.

Labarai masu alaka