Mata 100: Mai aiki ta mutu bayan an sa ta kwana da kare a waje

Malaysia Hakkin mallakar hoto Steven Sim Office
Image caption Adelina ta fuskanci cin zarafi daga iyayen gidanta a Malaysia

Wata 'yar aikin gida a Malaysia ta mutu bayan iyayen gidanta da ake zargi sun tilasta mata kwana tare da Karnunkan gidan a waje.

'Yar aikin gidan mai suna Adelina 'yar Indonesia ce da take aiki a gidan Penang.

Ana zargin iyayen gidanta da haramta ma ta abinci, tare da kin kai ta asibiti bayan raunikan da ta samu a jikinta.

An ceto Adelina a ranar goma na Fabrairu bayan wani makwabci ya kai karan halin da ta ke ciki ga wani dan siyasa mai suna Steven Sim.

Kuma ta rasu ne bayan an kai ta asibiti a ranar Lahadi.

Yanzu haka 'yan sandan Malaysia na tsare da uwar gidanta mai shekaru 36 da wani dan uwanta da ake zargi da aikata kisa, kamar yadda kafamfanin dillacin labaran kasar ya ruwaito.

Sannan 'Yan sanda na tsare da mahaifiyarsu mai shekaru 60.

Hakkin mallakar hoto Migrant Care
Image caption An ga raunukan da ba a yi musu magani ba a jikin Adelina

Mista Sim ya shaidawa BBC cewa rasuwar Adelina da halin da ta shiga daga iyayen gindanta abin takaici ne ga Indonesia.

Mista Sim ya tafi gidan da Adelina ke aiki a ranar Asabar domin binciken dalilin da ya yi sanadin ajalinta.

Ya ce Adelina ta ji jiki, sannan kuma ta samu munanan raunuka a hannunta.

"Adelina ta ce an tilasta ma ta bacci tare da kare na tsawon wata daya", kuma cikin watannin ba a bata abinci ko so daya ba, kuma ta fuskanci wulakanci", in ji shi.

Daraktan ofishin da ke kare 'yan Indonisia a ma'aikatar harakokin waje Lalu Mohammed Iqbal ya ce zuwa yanzu babu wani abu da aka gano da ya yi sanadin rasuwar Adelina, amma a cewarsa ana ganin raunukan da ta samu ne daga cizon kare, ko kuma rashin isasshen abinci ne suka yi ajalinta.

An fahimci cewa Adelina ba ta samu an kula da lafiyarta ba bayan raunukan da ta samu, wanda hakan ya sa ta kamu da wasu cututtukan da har suka karya garkuwar jikinta.

Hukumomin Malaysia sun ce ba za su ce komi ba game da al'amarin har sai 'yan sanda sun kammala bincike bayan da BBC ta tuntube su.

Amma Ministar harkokin wajen Indonesia Retno Marsudi, ta ce tana so a bi ma Adelina hakkinta.

Malaysia dai na daya daga cikin manyan kasashe a Asiya inda mutane ke zuwa aikin kwadago amma a kudaden da bai taka kara ya karya ba.

Akwai akalla 'yan Indonesia miliyan 2.5 da ke aiki a Malaysia kuma rabinsu na aiki ba tare da izini ba, in ji Mista Iqbal.

Sauran ma'aikatan kwadagon sun fito ne daga Myanmar da Philippines da Vietnam da Bangladesh da Laos da Cambodia da Sri Lanka da Thailand.

Hakkin mallakar hoto Por Cheng Han
Image caption Adelina ta kwana a baranda tare da karen iyayen gidanta