Firaminastan Ethiopia, Hailemariam Desalegn, ya yi murabus

Habasha Hakkin mallakar hoto AFP/Getty

Gidan talbijin na kasar Ethiopia ya sanar da cewa Firai Ministan kasar Hailemariam Desalegn, ya yi murabus.

Har yanzu ba a fadi dalilin yin murabus din nasa ba. Mista Hailemariam ya kuma sauka daga matsayin jagoran hadin gwiwar mulkin kasar.

Saukarsa daga mulki ta zo ne bayan watanni na zanga-zangar da 'yan adawar gwamnaati a yankunan mafi girma a Habasha, Oromia da Amhara su ka yi ta yi.

An kashe mutum 10 sannan mutane da dama sun ji rauni sakamakon zanga-zangar adawar da aka yi a baya-bayan nan.

Wakilin BBC Emmanuel Igunza, a babban birnin kasar Addis Ababa, ya ce gwamnati ta fitar da dubban 'yan adawa daga kurkuku a cikin 'yan makonnin nan, amma har yanzu ana ci gaba da zanga-zangar.

An yi ta gudanar da jerin zanga-zanga a Habasha da tahse-tashen hankula tun daga shekarar 2015, tare da masu zanga-zangar neman kawo sauye-sauye a siyasa da tattalin arzikin kasar, da kuma kawo ƙarshen cin hanci da rashawa.

Rikice-rikicen da ke gudana sun haifar da rarrabuwar kawuna sosai a cikin hadin gwiwar gwamnati, in ji Mary Harper, Editar Afirka ta BBC.

Ta kuma ce wasu daga cikin manyan masu fada a-ji na kasar sun fara ganin Firai Ministan kamar a matsayin wani wanda ba shi da karfi kuma bai iya jagoranci ba.

Halin da Habasha ke ciki a yanzu na da hadari ga dukkan yankin kusurwar Afirka, in ji 'yar jaridar, saboda ana ganin zaman lafiyar kasar a matsayin wani ginshiki na kawo zaman lafiya a yankin.

Labarai masu alaka