Mutum 5 sun mutu a hatsarin ayarin shugaban kasar DR Congo

President of the Democratic Republic of Congo, Joseph Kabila, holds a press conference for the first time in five years on January 26, 2018 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Kabila ya taimaka wa wadanda suka ji raunuka yayin hadarin

Mutum biyar ne suka mutu sakamakon hatsarin da wasu motocin ayarin shugaban kasar Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo suka yi da wata babbar motar dakon siminti.

Sojoji uku da farar hula biyu ne suka mutu daga ayarin shugaban kasar, a yayin da Shugaba Joseph Kabila ke komawa daga babban birnin kasar Kinshasa.

Wani mai magana da yawun shugaban kasar Yvon Ramazani, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wasu mutum 11 kuma sun jikkata.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake shekawa a lokacin, duk da cewa dai wasu rahotanni sun ce gudun da ayarin ke shararawa ne ya jawo hatsarin.

Wasu da suka shaida lamarin sun shaida wa gidan rediyon Okapi cewa tsananin gudun ayarin motocin ne ya jawo hatsarin.

Mista Ramazani ya ce, hatsarin, wanda ya faru a ranar Talata da yamma, ya faru ne a lokacin da wata babbar motar dakon suminti ta bugi daya daga cikin motocin ayarin shugaban kasar.

Shugaba Kabila yana komawa Kinshasa ne daga birnin Matadi ne mai tashar jiragen ruwa, inda ya je don kaddamar da wani ofishin kamfanin man fetur.

Ya kuma tsaya a wajen da hatsarin ya faru har sai da masu bayar da agajin gaggawa suka isa wajen, ya kuma duba yanayin da motar da za ta kwashe mamatan take.

Shugaba Kabila dai wanda ya hau mulki tun shekarar 2001, bayan da aka kashe mahaifinsa, yana fuskantar matsin lamba don ya sauka, tun bayan da wa'adin mulkinsa ya zo karshe a watan nuwambar 2016.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon yadda titunan birnin Kinshasa suka lalace

Labarai masu alaka