Beraye sun lalata gonakin shinkafa a Kebbi

Map of Kebbi

Hukumomi a jihar Kebbi da ke arewa maso gabashin Najeriya sun bayar da rahoton cewa beraye da kwari sun shiga gonakin shinkafa sun yi barna sosai, tare da lalata shuka.

Bayanai sun nuna tuni wannan matsalar ta fara saka wasu manoman watsi da noman a wannan shekarar.

Akwai fargabar cewa Najeriya na iya fuskantar karancin shinkafar da ake nomawa a kasar, sakamakon barnar da berayen suka yi a gonaki da dama a Kebbi daya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen samar da shinkafa a kasar.

Bayanai dai na nuna wannan lamarin ya fi kamari a yankunan kananan hukumomin jihar biyar da suka hada da Augie da Argungu da Bagudo da Dandi da Kalgo da Bunza da Suru.

Wani manomin shinkafar a garin Argungu Sanusi Adamu ya shaidawa BBC cewa matsalar ta soma ne tsawon watanni amma ta fi kamari ne a yanzu.

"Berayen sun yi wa kusan dukkanin manoman Argungu barna, da kuma kwari da ke lalata shinkafa" a cewar Malam Sanusi.

Ya kuma ce noman shinkafar ya ragu, saboda matalar berayen da kwari da suka addabi gonakinsu.

Sai dai kuma ma'aikatar gona a Kebbi ta ce tuni ta dauki mataki game da berayen da kwarin.

Alhaji Garba Dan dika kwamishin aikin gona na Jihar Kebbi ya ce tun da suka samu labarin makwanni biyu da suka gabata suka gabatar da bayanin matsalar ga Gwamnan Jihar.

Kwamishin nan ya ce an sayo maganin kwari da na kashe bera da za a yi feshi ta sama domin magance matsalar.

Sai dai hukumomin jihar sun ce dama akwai berayen, kuma noman shinkafar ne yanzu ya kasance abincinsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kebbi na cikin jihohin da ke kan gaba wajen noman shinkafa a Najeriya

Tuni dai gwamnatin Najeriya ke nazarin haramta shigo da shinkafa daga waje zuwa cikin kasar domin bunkasa noman shinkafar a cikin gida.

Gwamnatin Kebbi ta bayyana matsalar berayen da kwari a matsayin wata gagaruma wadda ka iya shafar samar da shinkafa a kasar ma baki daya.

Wannan kuma na zuwa ne a farkon shekara ta 2018, shekarar da gwamnatin kasar ta saka karshenta a zaman wa'adin da take fatan daina shigowa da shinkafa daga kasashen wajen bisa hasashen cewa kafin sannan jihohin irin jihar Kebbi sun kawo karfin iya samar da shinkafar da za ta wadatar da kasar baki daya.

Labarai masu alaka