Goron Ghana 'ya fi armashi' a Nigeria

Mutanen Najeriya sun fi jin dadin goron Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutanen Najeriya sun fi jin dadin goron Ghana

Wani mai sayar da Goro a Najeriya, Danladi Mai Goro, ya ce goron da ake shigowa da shi daga kasar Ghana ya fi armashi, ma'ana mutane sun fi son sa.

Mai sayar da goron ya shaida wa BBC cewa, yawanci goron kasar Ghana ake kawo wa Najeriya ana dasawa, kuma Ghana ta fi Najeriya yawan goron ma.

Kasar Ghana dai na shigo da goro Najeriya kusan kashi uku, da suka hada da jan daushe da dan Ankara wanda shi fari ne, sannan kuma da wani goron wanda bai kai daushe tsada ba.

Duk da bukatar goron da ake a ko da yaushe, a yanzu haka farashinsa ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Najeriya.

Danladi mai goro ya ce, farashin goron na tashi ne saboda wani sa'in ya kan yadu sosai, yayin da wani lokaci kuma sai a samu akasin haka.

Ya ce: "A bana gaskiya bai yi 'ya 'ya sosai ba," amma suna sa rai yanzu da alama ya dan fara toho sosai.

Danladi mai goro, ya ce suna sa rai nan da zuwa watanni hudu masu zuwa farashin goron zai yi sauki saboda zai wadata.

Akwai dai kasashe da dama da ke shigo da goro Najeriya baya ga Ghana, akwai Ivory Coast da kuma Saliyo.