'Yan bindiga sun kashe akalla mutum 35 a jihar Zamfara

Map of Zamfara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin gaggauta tura sojoji zuwa jihar Zamfara a arewa maso yammacin kasar da ke fama da ke matsalar 'yan fashi da barayin shanu.

Wannan na zuwa bayan wasu da ake zargi 'yan bindiga ne sun kashe mutane 35 a harin da suka kai a kauyen Birane cikin karamar hukumar Zurmi.

Maharan sun kai harin ne a kan babura, inda suka tsare wata mota da ke dauke da wadansu 'yan kasuwan jihar, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Daga nan ne sai suka yanka makogwaro direban kafin suka fara bude wa motar wuta, abin da ya jawo mutuwar dukkan mutanen da ke cikin motar.

Bayan faruwar wannan ne, sai 'yan bindigar suka tafi wata kasuwa suka fara harbi kan mai uwa da wabi, inda suka sake kashe wani mutum guda.

Zuwa yanzu dai, jami'an tsaro ba su bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba sanadiyyar hare-haren wanda ake zargin barayin shanu da kai wa.

Amma wasu mazauna yankin da al'amarin ya faru sun shaidawa BBC cewa mutane 35 aka kashe.

Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar ya yi Allah wadai da harin wanda ya danganta na marar imani da rashin hankali.

Shugaban kuma ya bukaci ministan tsaro ya kai ziyara jihar domin tantance halin matsalar tsaron da jihar take ciki.

Jihar Zamfara ta sha fuskantar hare-hare daga mutanen da ake zargi barayin shanu ne a baya.

A watan Nuwambar bara, akalla mutum 24 ne suka rasa rayukansu kuma aka cinnawa gidajen jama'a da dama wuta a jihar.