Bayani kan aikin hukumar zabe mai zaman kanta ta Nigeria

INEC Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ranar Juma'a ce ta kasance saura shekara guda cif a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya, idan komai ya tafi daidai kamar yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasar, INEC, ta tsara.

A farkon watan Janairun bana ne dai hukumar ta INEC ta fitar da jadawalin zabukan shekara ta 2019.

Majalisun dokoki na kasar dai sun yi wa dokar zabe kwaskwarima ta yadda za a sauya jerin zabubbukan, amma sai shugaban kasa ya rattaba mata hannu kafin ta fara aiki.

Daga yanzu zuwa lokacin, za mu rika kawo muku makala akai-akai game da wasu batutuwan da suka shafi zabe a Najeriya.

A wannan mako mun fara ne da jin ko menene aikin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa?

Ga bayanin wani kwamishina a hukumar INEC Malam Mohammed Haruna:

Amsa: Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ita ce wacce take zaune a Abuja take kuma gudanar da zabe ba tare da karbar umarni daga wajen kowa ba.

Tambaya: Wadanne irin ayyuka take yi ba ya ga gudanar da zabe?

Amsa: Babban aikin da muke yi shi ne na gudanar da zabe, kuma akwai yi wa masu zabe rijista, mu ne kuma muke yi wa jam'iyyu rijista. Saboda kundin tsarin mulkin kasar ya ce ba za ka gudanar da zabe ba sai kana mamba na wata jam'iyya.

Mu muke rijistar 'yan takara da jam'iyyu mu kuma gudanar da dukkan zabuka ban da na kananan hukumomi.

Tambaya: Idan aka gudanar da zabe aka kuma samu rikici tsakanin jam'iyya da jam'iyya, akwai inda hukumar zabe ke shiga don sasantawa ko kafa hujja?

Amsa: Kwarai da gaske. Ya danganta da irin rigimar, kotu na iya kiranmu tun da mu muke yi wa 'yan takara rijista. Kuma idan za su tsayar da masu takara muna zuwa sanya ido. Idan kotu ta bukaci jin ta bakinmu, mu kuma za mu bayar da rahotonmu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tambaya: Ta wacce hanya INEC ke samun kudadenta don shirya zabuka?

Amsa: Kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadin cewa kai tsaye za a ciro kudin shirya zabuka daga asusun gwamnatin tarayya, in dai mun kai kasafin kudi majalisa ta amince, shugaban kasa ya sa hannu, to kai tsaye za a ba mu kudin daga asusun gwamnati.

Mene ne bambancin hukumar zabe ta kasa da ta jiha?

Amsa: Hukumar zabe ta kasa ce ke tsara zabukan shiga majalisar wakilai da ta dattijai da na majalisar dokokin jihohi da na gwamnoni da na shugaban kasa. Amma zabukan kananan hukumomi kamar na Ciyaman da Kansiloli, to hukumar zaben jiha ce ke yi.

Da a lokacin mulkin soja, hukumar zabe ta kasa ce ke yi, amma da aka sake kundin tsarin mulki na 1999 sai aka bai wa jihohi wannan damar.

Tambaya: A misali yanzu idan hukumar zabe ta jiha ta shirya zabe, ake kuma zargin ba a yi wa wani bangare adalci ba, shin hukumar zabe ta kasa tana shiga cikin maganar?

Amsa: A'a, ba ruwanmu da wannan. Ba ruwanmu da zaben da hukumar zabe ta jihohi ke yi. Sai dai a wasu lokutan mu na taimaka musu da kayayyakin gudanar da zabe. Majalisar jihohi ne ke tsara musu dokoki. Mu kuwa majalisar wakilan tarayya da ta dattijai ke tsara mana dokokinmu.

Tambaya: Ko hukumar zabe na da wasu hanyoyin samun tallafi baya ga gwamnatin tarayya?

Eh hukumomi kamar na Majalisar Dinkin Duniya irin su UNDP da Commonwealth kan taimaka amma ba wai yta hanyar ba mu kudi ba. Su kan taimaka mana da masaukai da kudin zirga-zirga a lokutan da gudanar da bayar da horo ko wasu taruka. Ba Najeriya kadai suke wa haka ba su na yi wa kasashe da dama. Amma ba ma barin su shigo cikin abun da ya shafi harkar gudanar da zabe.

Sai ku dinga kasancewa da mu a rediyo duk bayan mako biyu da don jin bayanai game da hukumar zabe ta kasa da shirin zaben 2018.

Sannan kuna iya karanta bayanan a shafinmu na www.bbchausa.com, kuma za ku iya aiko da tambayoyinku kan abin da kuke son sani game da batutuwan.

Labarai masu alaka