Ko gwamnatin Nigeria na son kara farashin man fetur?

layin mai

Asalin hoton, Getty Images

Masu fashin baki sun fara tsokaci kan cewa da alama gwamnatin Najeriya na iya kara kudin litar man fetur a wani mataki na kawo karshen karancin man fetir din.

Kimanin wata uku ke nan 'yan kasar na fama da dogayen layuka a gidajen mai, ba ya da tsadar man.

A ranar Alhamis ne dai gwamnan jihar Bauchi Muhammd A Abubakar, wanda ya yi wa manema labarai bayani a karshen taron majalisar tattalin arzikin kasar, ya ce majalisar ta umarci daya daga cikin kwamiocinta karkashin jagorancin gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dan Kwambo, da ya yi duba kan farashin man fetir a kasashe masu makwabtaka da kasar.

Sannan kuma sai ya bayar da shawara dangane da farashin da ya dace a rinka sayar da litar man a Najeriyar.

Daga cikin bayanin da gwamna M.A Abubakar ya yi wanda ya fi daukar hankalin 'yan Najeriya shi ne inda yake fadin cewa daya daga cikin dalilan da suka janyo matsalar karancin man fetur din da ake fama a kasar taki ci taki cinyewa, ita ce yadda 'yan wasu 'yan kasuwa kan karkakatar da akalar man da aka ba su zuwa wasu kasashe masu makwabtaka saboda ya fi daraja a can.

Rahotanni dai na cewa Najeriya ce kasar da ake sayar da man fetur a farashi ma fi rahusa a Afirka.

Yadda masu sharhi ke kallon lamarin

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Bala Zaka, Masanin harkar makamashi a jihar Legas da ke kudancin Najeriya

"Kara farashin ba zai taimaka a magance karancin man fetur ba. Ana rayuwar kunci yanzu a kasar da kuma tsanani. Idan dai har gwamnati ta ce za ta dauki matakin kara kudin (tatsattsen lu'u-lu'u) man fetur, to gaskiyar magana ita ce a karshe gwamnati za ta nakasar da tattalin arzikin kasar nan, kuma komai zai durkushe.

Idan za ta bi wasu hanyoyin gara ta bi amma ban da karin farashin mai. Idan ba haka za a jefa Najeriya a wani yanayi da a karshe kowa sai ya ce da ya sani."

Ina mafita?

"Abun da ya kamata a yi shi ne a kara matatun man fetur, domin idan muka ga duba za mu ga cewa tun tsakanin shekarun 1965 zuwa 1989 a lokacin shugabannin da muke da su sun gina matatun mai hudu. Biyu a Fatakwal, daya a Kaduna, daya a Warrri.

"Amma tun daga 1990 zuwa 2018 ba a sake kara gina ko matatar mai daya ba. Daga lokacin zuwa yanzu abubuwa sun karu, kamar motoci da masana'antu.

"Abun da ya kamata ayi shi ne tun da akwai man a Najeriya, to a hako shi a naira, a tura shi matatu a naira, a tace shi a naira, a kuma sayar wa 'yan Najeriya a naira, mu yi amfani da nairarmu.

"Wannan zai taimaka ya raba mu da duk abun da ake magana a kan kudin kasashen waje.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An shafe wata uku ana wahalar man fetur a Najeria

To idan aka bi wadannan matakai gaskiya za mu iya farfo da arzikin Najeriya," in ji Bala Zaka.

'Gara a kara kudin man'

Wasu 'yan kasar dai na ganin gara a ce an yi mai gaba daya wato a kara kudin man idan har man zai samu maimakon karin bayan 'yan kasa sun gama jigata.

Sai dai ana ganin shugaba Buhari ne ba ya son yin karin, watakila saboda tausayin talaka ko kuma tsoron ka da a kalli gwamnatin da mai son kara kudin man fetir har karo biyu.

Gwamnain APC ce dai ta kara kudin man fetur jim kadan bayan hawanta, daga Naira 95 zuwa 145 ko wacce lita.