An sanya dokar ta baci a Ethiopia

habasha

Asalin hoton, Reuters

Gwamnatin Ethiopia ta sanar da sanya dokar ta baci a kasar, kwana daya bayan da Firai Ministan kasar ya yi murabus.

Wata sanarwa da gidan talbijin na kasar ya fitar, ta ce matakin ya zama dole ne saboda a rage yawan zanga-zangar adawa da gwamnati da ake ta yi a kasar.

an kashe gomman mutane an kuma ji wa wasu dama raunuka yayin da aka yi wani yajin aiki don neman a saki fursunonin siyasa.

Wannan ne karo na biyu da gwamnati ke sanya dokar ta baci domin shawo kan wannan rikici.

An fara sanya sanarwar ne a shafin Facebook na gidan talbijin din kasar. Sai dai ba ta fadi ainihin tsawon lokacin da dokar ta bacin za ta dauka ba, ko kuma ka'idojinsa.

Wannan mataki dai na zuwa ne kwana daya bayan murabus din Firai Minista Hailemariam Desalegn, ya sanar da cewa ya yi murabus saboda rikicin da kasar ke fuskantar.

Sai dai ana sa ran majalisar dokoki za ta dawo daga hutun da take yi don amincewa da murabus din nasa, wanda tuni jam'iyyun hadaka da ke mulki suka amince da shi.

An shafe shekara uku kasar habasha na fama da zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a yankuna daban-daban da suka hada da Oromia, wanda shi ne yanki mafi girma a kasar.

Daga cikin bukatunsu dai har da neman kawo manyan sauye-sauyen siyasa,da hakkin mallakar fili da sakin fursunonin siyasa.

A makon da ya gabata be, kasar ta saki daruruwan fursunonin siyasa da 'yan jarida, amma duk da haka an ci gaba da zanga-zangar.

A watan Oktobar 2016, gwamnati ta sanar da sanya dokar ta baci da ya dauki tsawon wata 10 ana yi.