Buhari ya gana da gwamnonin APC a Daura

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Femi Adeshina

Bayanan hoto,

Gwamnonin APC sun samu Buhari a Daura

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyarsa ta APC 18 a garin Daura jihar Katsina.

An yi ganawar tsakanin Buhari da gwamnonin a yau Juma'a, kamar yadda Femi Adeshina mai magana da yawun shugaban ya sanar tare da wallafa hotunan ganawar a shafin Facebook.

Sai dai kuma gwamnonin Yobe da Plateau da Ogun da Benue da Osun sun tura mataimakansu ne suka wakilce su a taron.

Wadanda suka halarci ganawar a Daura sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da na Jigawa Badaru Abubakar da na Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.

Sauran sun hada da gwamnan Imo Rochas Okorocha da gwamnan Bauchi Abubakar Muhammed da na Borno Kashin Shettima da na Edo Godwin Obaseki da na Kogi Yahaya Bello da Abubakar Sani Bello na Niger da kuma gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura.

Jam'iyyar APC dai na fama da rigingimun cikin gida tun bayan da ta lashe zaben shekarar 2015.

Yanzu haka rikicin APC a jihar Kaduna na ci gaba da ruruwa bayan da wani bangare na jam'iyyar ya yi ikirarin bude sabon ofis tare da shelar dakatar da wasu shugabanni a Jam'iyyar.

Wannan kuma na zuwa bayan rikici tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da mutumin da ya gaje shi, Abdullahi Umar Ganduje.

Dalilin rikice-rikicen jam'iyyar a wasu jihohi ne a makon da ya gabata shugaba Buhari ya kafa kwamiti domin sasanta 'ya'yan jami'yyar.

Tsohon gwamnan Legas Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Buhari ya nada a matsayin shugaban kwamitin da zai yi kokarin ganawa da sasantawa tare da inganta zamantakewar 'ya'yan jam'iyyar.