An umurci Facebook ya daina bibiyar mutane

Facebook

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Facebook na bibiyar mutanen da ba su mu'amula da shi

Kotun Belgium ta bukaci kamfanin Facebook ya dakatar da bibiyar mutane ba tare da izininsu ba.

Kotun ta bukaci kamfanin ya share dukkanin bayanan da ya tattara a kan mutanen da ba su amfani da Facebook.

Kotun ta yanke hukunci cewa Facebook ya saba doka ta hanyar tattara bayanan mutane ba tare da saninsu ba.

Hukumar da ke kare hakkin sirrin mutane a Belgium ta ce shafin Facebook ya karya dokarta ta hanyar amfani da Cookies domin bibiyar wasu shafukan intanet.

Facebook zai fuskanci tarar kudi $311,000 a rana idan har bai bi umurnin kotun ba.

Facebook ya ce zai daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.

Kotun ta ce ya zama wajibi Facebook ya dakatar da bibiyar mutane da kuma tatsar bayanan adadin da lokacin da mutanen ke amfani da intanet a Belgium.

Sannan dole Facebook ya yi watsi da dukkanin bayanan da ya tatsa ba bisa ka'ida ba.

Tun a 2015 ne aka zargi Facebook da bibiyar mutanen da suka ziyarci wasu shafukan intanet ko da kuwa ba mambobinsa ba ne.