Za a bada tukwicin kwai ga ma'aikatan da ke zuwa aiki da wuri

Za a ba wa ma'aikacin da ke zuwa aiki da wuri tukwicin kwai a Venezuela

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Za a ba wa ma'aikacin da ke zuwa aiki da wuri tukwicin kwai a Venezuela

Wani kamfani da ke daukar hayar masu gadi a Venezuela, ya yi alkawarin bayar da tukwicin kwai 144 a duk wata ga ma'aikatan da ke shiga mai kyau da kuma zuwa aiki a kan lokaci.

Kasar Venezuela dai ita ce kasar da tafi fama da matsalar hahhawa da tashi farashin kayayyaki a duniya, kuma ta shafe shekaru tana fama da kanfar abinci da magunguna.

Manajan kamfanin na Atlas Security, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, mutane da dama sun nemi aiki a kamfanin wanda yawancinsu a matsayin masu gadi a gonakin da ke yammacin jihar Zulia.

Shugaban kasar Nicolas Maduro, ya ce kasar ta samu kanta cikin wannan yanayi ne saboda matakan karya tattalin azrikin da Amurka ta dauka a kanta ne.