'Yan kunar bakin wake sun kashe mutum 17 a Konduga

'Yan kunar bakin wake Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari a Konduga da ke jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno Satomi Ahmed ya shaida wa BBC cewa mutum 19 ne suka mutu, ciki har da 'yan kunar bakin waken biyu.

A cewarsa, mutum sama da hamsin ne suka jikkata sakamakon harin, wanda aka kai a wata kasuwa da ke garin na Konduga, kuma tuni aka garzaya da su asibiti.

Ganau sun ce harin ya yi matukar muni.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai ya yi kama da irin wadanda kungiyar Boko Haram ke kai wa.

Hukumomi a Najeriya na cewa suna cin galaba a yakin da suke yi da Boko Haram, ko da yake kungiyar ta matsa kai hare-haren kunar bakin wake.

A farkon makon nan ne rundunar sojin kasar ta sha alwashin bayar da tukwuicin N3m ga duk wanda ya bayar da bayani kan yadda za a kama shugaban wani bangare na Boko Haram Abubakar Shekau.

Ta ce Shekau ya koma sa "kayan mata da hijabi" a kokarinsa na tserewa.

Rundunar sojin Najeriya ta sha yin ikirarin kama Abubakar Shekau amma daga bisani ya fito ya musanta.