An yanke wa mai fyade hukuncin kisa sau hudu a Pakistan

Zainab Ansari, who was murdered in Pakistan, aged six Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fyaden da aka yi wa Zainab ya jawo tur daga dukkan Pakistan

Wata kotun Pakistan ta yanke hukuncin kisa sau hudu kan Imran Ali, dan shekara 24, saboda samunsa da laifin fyade da kisan wata yarinya 'yar shekara shida a watan jiya.

An tsinci gawar Zainab Ansari a cikin bola a birnin Kasur da ke kudancin Lahore ranar tara ga watan Janairu.

Kisan nata ya jawo Allawadai daga dukkan fadin kasar, inda mutane suka yi zanga-zanga saboda zargin 'yan sanda da rashin daukar mataki.

Mutum biyu ne suka mutu sanadin zanga-zangar.

Mahaifin yarinyar ya halarci zaman kotun, wanda aka yi shi cike da jami'an tsaro.

An zargi mutumin da ya kashe Zainab da hannu a wasu kashe-kashe da cin zarafin kananan yara mata a yankinsu.

Mutane da dama ne suka bayar da shaidar da ke nuna cewa yana da laifi, kuma bincike kan kwayoyin halittar sun nuna cewa shi ne ya aikata laifin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An zargi Ali da aikata laifukan kan kananan yara
Hakkin mallakar hoto CCTV images
Image caption An nuna hotunan da aka dauka da kyamarar sirri wadanda suka nadi yadda ake jan Zainab

Lauyan da ke kare Ali ya janye daga shari'ar bayan da wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin.

An yanke masa hukuncin kisa saboda sacewa da yi wa yarinyar fyade da kuma kashe ta, da aikata ta'addanci da kuma yin luwadi, sannan an ci shi tara.

Wani shafin da ke bayar da labarai na intanet, Dawn, ya ce Ali yana da mako biyu da zai iya daukaka kara kan hukuncin da aka yi masa.

An matsa wa 'yan sanda lamba sosai domin su gano mutumin da ya kashe Zainab da sauran yaran.

Mahaifan Zainab sun ce 'yan sanda ba su dauki mataki kan batun ba a kwana biyar na farko da aukuwar lamarin.

Ranar 23 ga watan Janairu ne aka kama Ali.

Labarai masu alaka