An soma watsa labaran BBC a harsunan Igbo da Yarbanci a Nigeria

Members of the BBC Igbo and Yoruba teams in Lagos, Nigera
Image caption Za a rika watsa shirye-shiryensu a shafin intanet

Sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya kaddamar da sassa biyu gamasu jin harsunan Igbo da Yoruba a Nigeria da Afirka ta Yamma.

Za a rika watsa shirye-shiryensu a shafin intanet da shafukan sada zumunta, akasari ga masu amfani da wayoyin salula.

Ana amfani harshen Igbo a kudu maso gabashin Najeriya, yayin da ake amfani da Yarbanci a kudu maso yammacin kasar da kuma kasashen Benin da Togo.

Sabbin sassan na cikin wadanda Sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya kaddamar a shirinsa mafi girma tun shekarun 1940, sakamakon kudin da gwamnatin Birtaniya ta bai wa sashen a shekarar 2016.

Ana kadamar da sabbin sassa 12 na BBC a Africa da Asia jimulla.

Sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya soma fadada shirye-shiryensa a Nigeria - kasar da ta fi kowacce yawan mutane a Africa wacce ke da harsuna sama da 200 - ne a bara inda aka kaddamar da Sashen BBC Pidgin, domin mutanen da ke magana da turancin buroka.

Pidgin harshe ne da ake magana da shi, wanda ba shi da wani tsari na rubutu.

Su kansu ma'aikatan da za su yi aiki a harsunan Igbo da Yarbanci na BBC sun fuskanci kalubale na tsarin rubutu da harsunan ga masu karanta labarai - har sai da ta kai ga neman shawarwarin malaman jami'a.

"Yarbanci ka iya rikita matasa masu karatu saboda yana da kalmomi irin daya masu ma'ana daban-daban, don haka sai ai mu yi amfani da jimloli masu sauki wurin isar da sako a gare su," in ji editan Sashen Yarbanci, Temidayo Olofinsawo.

Kafofin watsa labarai na harsunan Igbo da Yarbanci ba su da yawa a Najeriya, don haka ne ake sa ran sassan biyu na BBC za su samu karbuwa a gida da wajen kasar.

Wannanne karon farko da za a rika wallafawa da kuma watsa labarai da harshen Igbo ga kasashen duniya," a cewar Adline Okere, edita a Sashen Igbo na BBC.

"Igbos are known for their entrepreneurial spirit - and they are spread all over the world," she says.

Wadanne labarai za su ba ku?

Sassan biyu za su rika bayar da labarai sau biyu a tsarin BBC Minute - labarai da rahotanni cikin murya a shafin intanet da shafukan zumunta.

Image caption Ma'aikatan Sashen Yarbanci na BBC

Shugabar Afirka ta Yamma ta BBC, Oluwatoyosi Ogunseye, ta ce za a mayar da hankali ne kan labarai sahihai wadanda suka shafi al'umma.

"Bayar da labarai da kuma tattaunawa da masu sauraro a harsuna Igbo da Yarbanci abu ne mai nishadantarwa," in ji ta.

"Muna da BBC Hausa [wadda aka fi sauraro a arewacin Najeriya] a shekaru aru-aru kuma mun ga tasirin hakan ga masu saurare.

"Najeriya na da al'adu da dama kuma haka ne ya sa BBC ta bai wa kowanne bangare damar jin ta bakinsa a kowacce kafa."

Labarai masu alaka