Mutum 66 sun mutu a hatsarin jirgin sama na Iran

Iran Tehran Semirom map

Kamfanin jiregen saman Aseman ya ce dukkan fasinja 66 da ke cikin jirginsa da ya yi hatsari a yankin da ke cike da tsaunuka na kasar Iran sun mutu.

Jirgin ya fado ne a yankin Zagros mai cike da tsaunuka a lardin Isfahan a lokacin da yake kan hanyarsa daga Tehran zuwa Yasuj da ke kudu maso yammacin kasar.

Ya bar Tehran da misalin karfe 05:00 a agogon kasar kuma ba a ji duriyarsa ba tun daga lokacin.

Wani jami'i ya ce rashin yanayi mai kyau ya hana kai agajin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru.

"An sanya dukkan hukumomin bayar da agajin gaggawa cikin shirin ko-ta-kwana," in ji wani kakakin hukumar bayar da agaji.

Har yanzu dai hukumomi ba su ce komai kan mutanen da lamarin ya hada da su ba.

An yi amannar cewar jirgin samfurin ATR 72-500 ya shekara 20 ana amfani da shi.

Rahotanni sun ce akwai fasinjoji 60 a cikinsa, da matukan jirgi biyu da ma'aikatansa biyu da kuma jami'an tsaro.

Labarai masu alaka