Iceland: Za a hukunta wanda ya yi wa dansa kaciya

Za a sanya dokar hana kaciyar maza a Iceland Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Za a sanya dokar hana kaciyar maza a Iceland

Wani shugaban addinin musulunci a Iceland, ya yi alawadai da shirin da ake yi a kasar na hana kaciyar maza a matsayin wani yancin da mutane suke da shi na yin addininsu.

Ahmad Saddeeq, wanda limami ne a wata cibiyar raya addini da kuma al'adu a kasar, ya shaidawa BBC cewa, yin kaciya na daga cikin koyin addinin musulunci, dan haka batun hana wa sam bai dace ba.

Wani kudurin doka da ke gaba majalisar dokokin kasar a yanzu, ya tanadi hukuncin daurin shekara shida ga duk iyayen da aka samu da yi wa 'ya'yansu kaciya.

Wata likita na son a halatta kaciyar Mata

Tsoron kaciya ya hana 'yan mata komawa gida a Kenya

Kasar Iceland, ta zamo kasa ta farko a tarayyar turai da za ta fara bullo da doka a kan daina kaciyar maza.

A cikin kudurin dokar, an bayyana cewa yawanci ana yi wa yaran kaciya ne a gida kuma ba mamaki ana amfani da kayan aikin da ba a tsaftace su ba.

Musulman da suke kasar dai tsiraru ne.