Taron addu'o'in jagoran 'yan adawa a Zimbabwe

Taron adu'oin da aka yi a wani coci da ke Harare, ya samu halartar daruruwan mutane daga sassan kasar. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taron adu'oin da aka yi a wani coci da ke Harare, ya samu halartar daruruwan mutane daga sassan kasar.

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya mika ta'aziyyarsa bisa ga rashin da aka yi na jagoran 'yan adawa, Morgan Changirai, wanda ya mutu sakamakon cutar kansa a makon da ya gabata.

Mr Mnangagwa, ya bayyana marigayin a matsayin wani muhimmi a siyasar kasar wanda kuma ya dace a rinka tunawa dashi a tarihin kasar.

Daga nan ya yi kira ga al'ummar kasar da su hadu domin nuna alhininsu ga babban rashin da aka yi.

Taron aduu'oin da aka yi a wani coci da ke Harare, ya samu halartar daruruwan mutane daga sassan kasar.

Kazalika daruruwan magoya bayan 'yan adawar kasar sun taru a wajen cocin, sanye da jajayen kaya, launin jam'iyyarsu.

A ranar 15 ga watan Fabrairu ne Allah ya yi wa Tsvangirai rasuwa yana da shekara 65 a duniya.

A ranar Talata ne za a binne gawarsa a kauyensa da ke Buhera.

Labarai masu alaka