Hotunan yadda ake rayuwa bayan annobar Ebola

Shekara hudu kenan tun bayan da aka ba da rahoton barkewar cutar Ebola a kasashen Liberia, Guinea da Saliyo da ke Yammacin Afirka.

Mai daukar hotuna Hugh Kinsella Cunningham ya koma kasar domin duba rayuwar mutanen da wannan annoba ta shafa.

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Mutane da cutar ta kashe lokacin da ta barke a 2014 sun zarce mutanen da ta kashe tun lokacin da ta soma barkewar a 1976.

Cutar ta fi yin tasiri a yankunan talakawa irinsu yankin Liberia, inda, ga mutane da dama, samun abincin da mutum zai sa a bakin sallati ma ba karamin aiki ba ne.

West Point wani yanki ne mai cike da jama'a a birnin Monrovia. An gudanar da tarzoma lokacin da gwamnati ta rufe yankin sannan ta killace mutane da suka kamu da cutar.

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

'Yan sanda sun kashe jikan Eva Nah lokacin da yake zanga-zanga saboda killace mutane da gwamnati ta yi. "Babu abin da yake son yi kamar buga tamaula da kuma zaman makanike," in ji ta. "Mahaifi da mahaifiyarsa sun mutu don haka ni kadai ce danginsa."

Shekaru bayan mutuwar tasa, an bai wa Eva diyyar kisansa abin da ya ba ta damar tura sauran yara hudu na danginta makaranta.

'Yar uwar Rita Carol na cikin wadanda Ebola ta kashe. Ta taba sayar da abinci a kan wata hanya da ke West Point sai dai ta tara kudin da ta sayi firinji sannan ta soma kasuwancin kankara, inda take fatan rayuarta za ta inganta.

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Etta Roberts ma'aikaciyar jinya ce a asibitin Kahweh da ke gabashin Monrovia. Akasari tana duba marasa lafiya 10 wadanda ke fama da zazzabi da kuraje.

Mutumin da ya bude asibitin, Reginald Kahweh, ya bude cibiyar kula da masu cutar Ebola bayan ya mahaifansa sun mutu sakamakon cutar, yana mai cewa: "Dole kowa ya dauki matakin da zai inganta al'uma… an gina wannan waje ne domin tunawa da wadanda suka mutu."

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Annobar ta Ebola ta ggirgiza tsarin kiwon lafiyar Liberia inda kayan aiki suka kare. Dama dai kasar ba ta da ingantaccen tsarin kiwon lafiya saboda yakin basarar da aka kwashe shekara 14 ana yi.

Don haka ne ake sanya ido sosai kan yankuna kamar West Point inda ma'aikatan cibiyar kula da lafiya ta kasar ke sa ido ba dare ba rana ko da wani abu zai faru.

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

J Roberts na zaune a yankin na West Point wanda ke fama da zaizayar kasa. Ya soma kasuwanci bayan matarsa ta mutu sakamakon Ebola. "An kona gawar matata, ba binne ta aka yi ba don haka ji nake kamar ba zan sake ganinta ba. Na yanke shawarar ba da kulawa ga 'ya'yanmu hudu," in ji shi.

Yana sayar da ruwan zafi. Wannan sana'a na da matukar muhimmanci saboda rashin tsaftar da ake fama da ita a cikin al'umarsu.

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Duk da tagomashin da tsarin kiwon lafiyar kasar ya samu da kuma fatan mutanen da lamarin ya shafa ke da shi na ci gaba da gudanar da rayuwa, da dama daga cikin ma'aikatan da suka rika binne gawarwaki na cikin tsaka mai wuya.

Akasarin ma'aikatan talakawa ne shi ya sa suka yi murnar da aka ba su aikin.

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Gwamnati ta dauki Mohammed Kanu a matsayin mutumin da zai rika binne gawarwakin ba tare da matsala ba. Bai sake samun wani aiki ba shi ya sa ya koma kulka da tsirrai.

Bukukuwan da aka rika yi lokutan binne gawarwakin sun taimaka wurin yada cutar kuma an rika tsangwamar mutane da dama suka yi aikin binne gawarwaki.

Morla Kargbo, wani tsohon ma'aikacin binne gawa, ya yi bayani: "Mutane ba sa son ba mu hayar gida saboda sun san mun yi aikin binne mutanen da suka kamu da Ebola."

Asalin hoton, Hugh Kinsella Cunningham

Dukkan hotunan nan na Hugh Kinsella Cunningham ne.