Dakarun Syria sun yi wa 'yan tawaye luguden wuta

Luguden wutar da dakarun gwamnatin Syrian suka yi a Gabashin Ghouta da ke wajen birnin Damascus, wanda ke hannun 'yan tawaye ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, in ji masu fafutika.

Kananan yara na cikin wadanda aka jikkata

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Kananan yara na cikin wadanda aka jikkata

Kungiyar the Syrian Observatory for Human Rights ta ce an kashe akalla farar hula 98, ciki har da kananan yara 20, sakamakon luguden wutar da aka yi ta sama da roka ranar Litinin.

Kungiyar, wacce ke da mazauni a Birtaniya, ta kara da cewa an jikkata mutum akalla 470, wasunsu ma na halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Jami'an majalisar dinkin duniya sun ce lamarin da ke faruwa a kasar ya wuce abin da hankali zai dauka, suna masu yin kira a tsagaita wuta.

Mutum kusan 400,000 be ke zaune a Gabashin Ghouta, wanda aka yi wa kawanya tun shekarar 2013.

Anyi amannar cewa rundunar sojin Syria na shirin soma kai hare-hare ta kasa a yankin.

Yankin shi ne tunga ta karshe da ke hannun 'yan tawaye a wajen birnin Damascus.

Dakarun Syria sun matsa kaimi a yunkurin da suke yi na kwace yanki, inda rahotanni ke cewa sun kashe daruruan mutane tare da jikkata da dama.