An tilasta wa 'mayu' shan fitsarin mutum a India

Ana zargin matan biyu da maita
Image caption Jami'ai a yankin sun bai wa matan wani kati bayan samun labarin abin da ya faru

'Yan sanda a India sun kama mutum 11 da laifin cin zarafin mata biyu a kudancin jihar Jharkhand sakamakon zargin su da maita.

An yi wa matar mai shekara 65 da 'yarta mai shekara 35 tsirara, tare da aske musu gashi sannan aka zagaya da su tituna har da kasuwannin kauyen, tare da tilasta musu cin kashin bil adama.

Matashiyar ta shaida wa BBC cewa ana zargin ta da mahaifiyarta da yada wata cuta a kauyen.

Zargin maita dai ba wani sabon abu ba ne a wasu yankunan kasar India, musamman ga mata.

Kwararru sun ce camfin da mutane ke yi kan maita na kara sanya rayuwar mutane cikin hadari, wasu matan da maza suka mutu kan fuskanci irin wannan matsalar musamman idan ana son cinye musu gadon filaye ko kuma gonaki.

Uwa da 'yar sun tafka kuskuren tuntubar wani likita da bai kware ba a lokacin da wani dan uwansu ya mutu, shi kuma ya dora alhakin mutuwar akansu.

''Washegari ne aka hukunta mu,'' in ji 'yar matar.

Duk da sun ki amincewa da zargin da ake musu, sai da 'yan uwansu suka taru aka tasa keyarsu zuwa wani fili aka kuma watsa musu fitsari a fuska, tare da tilasta musu hadiye fitsarin ta hanyar dura.

Mutane sun taru suna kallonsu da yin tofin alla-tsine a lokacin da aka zagaya da su kasuwa tsirara.

Matan biyu sun sha bakar wahala, babu kuma wanda ya zo don taimaka musu.

'Yan sandan yankin sun ce sun fara wani shirin gangamin wayar da kan al'umma, musamman na yankunan karkara, don magance sake faruwar haka nan gaba, sannan sun bai wa matan kariya.

Labarai masu alaka