Dan wasan Kano Pillars Chinedu Udoji ya mutu a hatsarin mota

Chinedu Udoji Hakkin mallakar hoto Chindeu Udoji/Facebook
Image caption Chinedu Udoji ya mutu ya bar mace daya da yara biyu

Dan wasan tsakiya na kulob din Kano Pillars, Chinedu Udoji, ya mutu sakamakon hatsarin mota.

Mai magana da yawun kungiyar Idris Rilwanu Malikawa Garu, ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi da daddare a kan titin Bompai da ke birnin Kano.

Garu ya ce, "Motar Udoji ta bugu ne a jikin ginin shatale-talen Independent Way, a kan hanyarsa ta komawa gidansa da ke unguwar Badawa, bayan ya kai wa wani abokinsa dan wasan tawagar Enyimba ziyara a otal.

Udoji dai shi kadai ne a cikin motar yayin da hatsarin ya faru.

Udoji na cikin tawagar Kano Pillars a wasan da suka buga da Enyimba inda aka tashi 1-1 a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Kulob din Kano Pillars ya ce yana aiki kan duk wasu takardu da ake bukata don kai gawar zuwa kauyen mamacin don binne shi.

Udoji dai ya mutu ya bar mata daya da 'ya'ya biyu.

Karin bayani