Nigeria: An yi jana'izar Sheikh Abubakar Tureta

Tureta Hakkin mallakar hoto Nurah Ringim
Image caption Sheikh Tureta ya mutu yana da shekara 74 a duniya

Allah ya yi wa sanannen malamin nan na addinin musulunci da ke Kaduna a arewacin Najeriya Sheikh Abubakar Tureta rasuwa.

Malamin ya rasu ne a ranar Lahadi a Asibitin Garkuwa da ke Kaduna.

Tuni dai aka yi jana'izar marigayin a ranar Litinin da safe a gidan sa da ke Tudun Wada layin Kosai.

Ya mutu yana da shekara 74 a duniya.

An haifi Sheikh Abubakar Tureta ranar biyar ga watan Janairun 1944, kuma dan asalin jihar Sokoto ne da ke arewa maso yammacin kasar.

Ya mutu ya bar mata uku da 'ya'ya 39 da kuma jikoki 85.

Malamin yana daga cikin jiga-jigan malamin kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Ikamatus Sunnah.

Ya taba rike shugabancin majalisar malamai na tsohuwar jihar Sokoto.

Hakkin mallakar hoto Kaduna State government
Image caption Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai na cikin mutanen da suka sallaci gawarsa

Labarai masu alaka