'Gyaran motar Boko Haram ya sa mun shekara 8 cikin ukuba'

Nigerian Islamist extremist group Boko Haram pictured with the leader of the Nigerian Islamist extremist group Boko Haram, Abubakar Shekau (C). Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban wadanda ake zargi da Boko Haram suna tsare

A lokacin da wasu kanikawa masu gyaran mota 'yan tagwaye Taye da Kehinde Hamza suka karbi gyaran wata mota a shagonsu da ke jihar Bauchi a Najeriya cikin shkarar 2010, ba su taba tsammanin za su shafe shekara bakwai cikin ukubu ba.

Ashe ba su san cewa motar ta wani mayakin boko Haram ba ce, kuma gyaranta da suka yi ya sa aka kama 'yan biyun.

Sai da suka shafe shekara takwas kafin su samu 'yancinsu, inda aka sake su tare da wasu mutum 524 da ake tuhuma da ayyukan ta'addanci.

Labarinsu daban yake daga cikin dumbin mutanen da ake ci gaba da yi musu shari'a.

Alkalai hudu ke sauraron kararrakin tun Litinin din makon da ya gabata a garin Ka'inji da ke jihar Naija a tsakiyar kasar.

Zuwa yanzu dai wadanda ake sake sakamakon rashin kwararan shaidu sun fi yawa a kan wadanda aka samu da hannu a kungiyar aka kuma yanke musu hukunci.

Ta auri dan Boko Haram tana da shekara 11

Mafi yawan wadanda aka sallama a makon da ya gabata sun hada da yara da tsofaffi.

Wasu kuwa kamar Taye da Kehinde sun kasance a tsare ne tun shekarar 2010.

Mariam Mohammed kuwa 'yar kabilar Shua Arab daga jihar Borno State, sojoji ne suka kama ta a yayin da take neman tserewa zuwa dajin Sambisa - sansanin 'yan Boko Haram a shekarar 2014.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan yarinyar na daya daga cikin miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu

Ta kallafa ran son zuwa dajin ne aka kuma aurar da ita ga wani mayakin kungiyar a lokacin da take da shekara 11, a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar shari'a ta Najeriya.

A makon da ya gabata ne, ta bayyana a kotu da jaririnta dan wata uku.

Har yanzu dai ba a san irin tasirin da dadewar da suka yi a tsare ta yi musu ba.

Ma'aikatar shari'ar ta ce wasun su suna fama da ciwon hauka, duk da cewa ba a tabbatar da ko suna tare da ciwon ba ne tun kafin a tsare su.

A shari'ar da aka yi a watan Oktobar 2017, an saki fiye da mutum 400 da ake zargi, inda aka yankewa 45 hukuncin dauri saboda rawar da suka taka a kungiyar Boko Haram, wadda ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 20,000 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.

Wanda ya kitsa sace 'yan matan Chibok

Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa za a kai wadanda aka sallama din cibiyar sauya tunani kafin daga bisani a mika su ga muhallansu.

Amma a yayin da wadannan alkalan suke kokarin ganin an yankewa wadanda ake tuhuma hukunci, akwai kuma wasu mutum 5,000 din sa suke jiran a saka musu ranar da za a yi tasu shari'ar.

Alkalan sun samu mutum 205 da laifukan da suka shafi ta'addanci, da suka hada da 'kitsa' sace 'yan matan sakandaren Chibok.

Haka kuma alkalan sun wanke Modu Maina daga tuhumar shiga kungiyar Boko Haram.

Tun da farko alkalai sun samu Haruna Yahaya, wani mai shekara 35 da hannu wajen kitsa sace 'yan matan sakandaren Chibok a 2014, duk da ya musanta cewa bai aikata hakan bisa son rai ba.

A ranar Juma'a, suka kara masa tsawon zama a gidan yari saboda shirya sace 'yan matan.

An yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara 30.

Ma'aikatar shari'ar kasar ta ce an dage shari'ar wasu mutane 73 sai nan gaba.

Amma a yayin da ake sa ran irin wadannan hukunci za su zama sakayya ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, kungiyar da ke kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta saka ayar tambaya kan yadda ake gudanar da shari'ar.

Kungiyar ta sha gabatar da hujjoji da ke nuna yadda dakarun tsaro suka tsare daruruwan matasa a matsayin mayakan Boko Haram ba tare da wasu kwararan hujjoji ba.

Hukumomin Najeriya sun sha nanata cewa ana yi wa wadanda ake tuhuma adalci a wajen gabatar da shari'ar da kuma samar musu lauyoyin da ke kare su.

Labarai masu alaka