Wigan ta fitar da Man City a FA

Wigan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karo na uku ke nan da Wigan ke fitr da City a FA a kaka shida

Wigan Athletic ta taka wa Manchester City burki inda ta yi waje da ita a gasar FA a zagaye na biyar da suka fafata a daren litinin.

Will Grigg ne ya ci wa Wigan kwallo a ragar Manchester City ana saura minti 11 a tashi wasan.

Wigan da ke buga gasar lig one mataki na uku a Ingila ta samu sa'ar fitar da City ne a FA bayan jan katin da aka ba dan wasan City Fabian Delph tun kafin hutun rabin lokaci.

Karo na uku ke nan da Wigan ke fitar City a gasar FA a kakar wasanni shida.

Kungiyoyin premier uku ke nan suka sha kashi a gidan Wigan bayan doke Manchester City.