'Saura kiris sojojin Nigeria su kama Shekau suka janye'

Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ce ta kai hari Maiduguri da wasu garuruwa a jahar Borno cikin 'yan kwanakin nan
Bayanan hoto,

Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ce ta kai hari Maiduguri da wasu garuruwa a jahar Borno cikin 'yan kwanakin nan

BBC ta samu labarin cewa saura kiris sojojin Nigeria su kama jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a wani farmaki da aka dakatar da su.

A wani faifen bidiyo da BBC ta samu daga hannun wasu da ke fafutika tare da sojojin Najeriyar, an ga yadda sojojin ke kai wa da komowa a wasu sansanoni na wucin gadi a dajin Sambisa.

Sai dai bayan kwana hudu da dakatar da sojojin daga ci gaba da kai farmakin, mayakan Boko Haram cikin motoci dauke da abubuwa masu fashewa sun kai wa sojojin hari.

An kashe sojojin Najeriyaa da na Kamaru bakwai wasu kuma da dama suka samu raunuka inda kuma aka lalata motocin sojojin da dama.

Sai dai mako guda bayan sojojin sun shiga sansanin da Shekau yake boye sun tarar ya riga ya tsere.

A halin yanzu rundunar sojin Nigeria ta ce za ta bayar da takuicin dala $8,000 ga duk wanda ya bata bayanai da za su kai ga kamo jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Rundunar sojin Najeriya dai ta sha nanata cewa ta kama ko ta kashe 'yan kungiyar, inda kuma a wani taron manema labarai a Maiduguri, rundunar ta zayyana makaman da ta ce ta kwace daga mayakan Boko Haram.