An kama mutumin da ya ce kiran sallah na damunsa a Saudiyya

Tsokaci nasa ya janyo masa caccaka daga wurin masu amfani da shafukan intanet.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsokaci nasa ya janyo masa caccaka daga wurin masu amfani da shafukan intanet.

Hukumomi a Saudiyya na binciken wani marubucin kasar bayan da ya ce masallatai sun yi yawa kuma kiran sallah na damunsa.

Binciken ka iya sa wa a hana mutumin, Mohammed al-Suhaimi, fitowa a kafafen watsa labarai ya yi magana.

Mohammed al-Suhaimi ya soki yadda ake gudanar da kiran sallah, yana mai cewa yawaita kiran sallar da kuma yadda masallatai daban-daban ke amfani da amsa-kuwwa (lasifika) wurin yin kiran yana hana mutane bacci da kuma damun kananan yara.

Marubucin, wanda ya yi suna wajen sassaucin ra'ayi, ya yi tsokacin ne lokacin da yake hira da wani gidan talbijin na kasashen Larabawa.

Tsokaci nasa ya janyo masa caccaka daga wurin masu amfani da shafukan intanet.

A baya dai, hukumomin Saudiyya sun sanya wasu matakai da suka umarci a rika rage karar lasifika lokacin kiran sallah.