Nigeria: El-Rufai 'ya rushe gidan Sanata Hunkuyi'

Sai dai Gwamna El-Rufai ya ce an rushe gidan ne saboda ya saba ka'idodjin gine-gine.

Asalin hoton, TWITTER/HUNKUYI

Sanatan da ke wakiltar jihar Kaduna a majalisar dattawan Najeriya Suleiman Hunkuyi, ya yi zargin cewa gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya rushe gidansa da ke jihar.

"Da sanyin safiyar yau [Talata] gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da kansa ya tuka motar rusau tare da rakiyar tankokin yaki inda suka rushe gidana da ke lamba 11B a kan titin Sambo.

"Wannan shi ne iyakar wulakanci da kuma rashin rashin ya kamata, wanda ba a taba ganin irinsa ba a jihar Kaduna," a cewar Sanata Hunkuyi, a wani sakon Twitter da ya wallafa.

Sai dai Gwamna El-Rufai ya ce an rushe gidan ne saboda ya saba ka'idojin gine-gine.

Wani sako da ya wallafa a shafin gwamnan Kaduna na Twitter ya ce: "An rushe wani gida a safiyar nan saboda ya keta dokokin gine-gine da kuma harajin kasa tun shekarar 2010.

"An mika filin da aka rushe hannun hukumar gine-gine domin mayar da shi wurin shakatawa."

Hotuna da bidiyon da Sanata Hunkuyi ya wallafa ba su nuna Gwamna El-Rufai cikin motocin da ya yi ikirarin cewa yana ciki ba.

Gwamnan da dan majalisar ta dattawa sun sha fama da rikicin siyasa, lamarin da wasu ke gani shi ne musabbabin rusa gidan sanatan.

Gidan da aka rusa shi ne ofishin bangaren da ke hamayya da Gwamna El-Rufai na jam'iyyar APC.

Masu sharhi na gani rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnan da wasu manyan 'yan siyasar jihar, ciki har da Sanata Shehu Sani da Honourable Isa Ashiru, ka iya kawo wa jam'iyyar APC matsala a zaben 2019.

Asalin hoton, TWITTER/HUNKUYI