Ana bincike kan yadda kafafen sada zumunta da wayoyi ke yi wa matasa illa

Wata matashiya rike da wayar salula a hannun ta

Asalin hoton, Getty Images

Shin ka damu da illar da shafukan sada zumunta na internet, da hasken fuskar wayar salula ke yi ga rayuwar matasa?

Idan haka ne, ga wata dama ta samu don kuwa 'yan majalisu na gudanar da bincike kan hakan da lalubo hanyoyin magance su.

Kwamitin kimiyya da fasaha ya sanar da fara wani bincike kan hakan, musamman ta fuskar lafiyarsu.

Kwamitin ya bukaci jin ta bakin matasan da kansu, da malaman makarantu da kuma matasa ma'aikata.

Shugaban kwamitin Norman Lamb, ya ce ya na da muhimmanci a bincika don gano alfanu ko kuma illar hakan.

"Shafukan sada zumunta na zamani da wayoyin komai da ruwanka, sun zamewa matasa wani abu da dole su yi amfani da shi har ma da yara kanana,' in ji shi.

Ya kara da cewa: "Mu na son sanin girman matsalar, da ware alfanu da akasin hakan don mu san ta inda za mu shawo kan matsalar kafin wankin hula ya kai mu dare.

Sannan mu san matakan da ya kamata mutane su fara dauka, don kare lafiyarsu, anan ina magana akan matasa da yara har da manya.''

"Za mu so jin ta bakin matasa, da 'yan makaranta, da gwamnati kai har da ma'aikatun da sauransu,'' in ji Mista Lamb.

Kwamitin dai zai mayar da hankali ne don jin cikakken bayanin yadda matasa suke ji idan su na yawan kallon hasken fuskar wayoyinsu, da abin da suke karauwa da su a shafukan.

Su ma malaman makaranta za mu so jin ta bakinsu, da kungiyoyin matasa wadanda su muke son hada karfi da karfe don magance illar da duniyar yanar gizo ka iya yi ga lafiyarsu.''

Cikin batutuwan da 'yan majalisun za su amince da su sun hada da:

  • alfanun da shafukan sada zumunta ke yi ga wadanda ke amfani da su, ciki har da samar da wata manhaja da za ta kula da lafiyar masu amfani da shafukan.
  • illollin da wayar komai da ruwanka ke yi na zahiri da boye, ciki har da matakan da za a bi don kaucewa hakan da samar da wani abu da zai zama kamar tunatarwar lokacin dauke ido daga fuskar wayar ya yi.
  • karin matakan rage hasken fuskar waya, ciki har da bayyana illar kallon kurulla da ake yi wa fuskar wayar.
  • wadanne madannai, ko alamu za a sanyawa wayoyin da ke nuna illa ko akasin hakan.
  • a karshe wanne bangare ya kamata a fi maida hankali a kai a binciken da ake son yi da matakan kariya na dindindin, da kuma amfani da su.
Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kwamitin zai bai wa mutane damar da aiko shawara ko korafi a rubuce, su na da damar yin rubutun da ya kai kalmomi 3,000 amma kar ya wuce hakan, daga yanzu zuwa 6 ga watan Afirilu.

Wani rahoto da hukumar ilimi ta wallafa a shekarar 2017, ya nuna kashi 95 cikin 100 na yara 'yan shekara 15 a Birtaniya sai sun yi amfani da shafukan sada zumunta kafin su tafi makaranta ko bayan sun tashi daga makarantar.

Sannan kuma rabin yara 'yan shekara 9 zuwa 16 na amfani da wayoyin komai da ruwanka a ko wacce rana.

A watan Janairun shekarar nan kwamishinar yara ta birnin London, Anne Longfield, ta yi gargadin cewa matakin da ake so a dauka na takaita amfani da wayoyin salula ko shafukan sada zumunta zai kawo nakasu ga 'yan makarantar firamare da sakandare, saboda su na amfani da shafukan don amfanin kansu da kuma fadada ilimi.

Rahoton ya yi nazari kan illar shafukan sada zumunta na zamani kan wasu yara 'yan shekara 9 zuwa 12, ya nuna yawancin yaran kan wallafa wani abu ne don su samu wadanda za su so shafukan na su da tsokaci kan wani rubutu da suka yi da kuma su ka wallafa a shafin.