An kama wani dauke da zinarin sama da N360m a Kenya

Zinari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jami'an tsaron Kenya sun kame wani dan Tanzania da zinarin da darajarsa ta kai dala miliyan daya, kwatankwachin sama da naira miliyan 360.

An kama mutumin ne mai shekara 45 a tashar jirgin sama ta Jomo Kenyatta a Nairobi, a lokacin da yake kokarin shiga jirgi zuwa Dubai a ranar Juma'a.

Nauyin zinarin da mutumin ke dauke da shi ya kai kilo 32.

Rahotanni daga Kenya sun ce jami'an haraji ne suka kama shi, bayan an tsegunta mu su labari game da mutumin da ke dauke da zinarin.

Yanzu zinarin na hannun jami'an kwastam na Kenya a yayin da 'yan sanda ke ci gaba da gudanar da bincike.

Labarai masu alaka