An fara hada agogon da zai yi aiki shekaru aru-aru

Karafan da masu ziyara ke wanawa masu kama da kacar keke da ke karawa baitirin agogon karfi

Asalin hoton, Eyewire Inc

An fara aikin hada wani agogo da zai aiki a shekaru aru-aru ba tare da bil'adam sun sanya hannu a gyaran shi ba.

Agogon mai shekara 10,000 na Cibiyar Long Now Foundation ne, wata cibiya mai zaman kanta wadda ke rajin tabbatarda dorewar tunanin bil'adama.

Kamfanin Amazon mallakar Jeff Bezos, shi ya samar da agogon, da aka girke shi a kusa da tsaunukan da ke hamadar Texas.

Babu takamaiman lokacin da aka dauka wajen yin agogon, da lokacin da aka girke shi.

Wanda ya kera agogon da hannunsa shi ne Danny Hillis dan Amurka, kuma a shekarar 1995 ne aka wallafa bayanai kan agogon.

A cikin agogon an yi amfani da wata fasaha da ke bai wa agogon damar kadawa ko bugawa sau daya a shekara, da kuma wani hannu da baya motsi sai bayan shekara 100 da kuma wata kara da sai bayan shekara 1,000 ake jin ta.

Haka kuma, agogon ya samu karfin yin aiki ne idan ya na zuko sauye-sauyen yanayin da duniya ke zuwa da su lokaci zuwa lokaci. Kuma wannan ne ke karawa sauran madannan da ke jikin sa karfi.

Sai dai kuma ba ya iya adana makamashi mai karfin da zai sa agogon ya dinga aiki a ko wanne lokaci har sai masu ziyara sun kunna agogon sannan sun dinga tura wata kaca mai kama da tayar keke ta haka ne batirin ya ke kara karfi, kamar yadda cibiyar Long Now Foundation ta bayyana.

A ranar talata ne Bezos, ya wallafa wani hoton bidiyo a shafin twitter kan yadda aikin gyaran agogon ya ke gudana.

Tuni aikin gyaran agogon ya dauki hankalin mashahuran mutane, baya ga mista Bezos na kamfanin Amazon wanda ya bada tallafin dala miliyan 42 don yin gyaran.

Shi ma wani fitaccen mawaki dan Birtaniya Brian Eno, ya kera wani abin kida da zai dinga fitar da sauti daban-daban a kowacce rana, kuma zai dauki shekara 10,000 ya na aiki ba tare da ya tsaya ba.

Cibiyar Long Now Foundation, ta ce masu yawon bude ido suna da damar kai ziyara hamadar Texas domin ganin yadda aikin gyaran agogon ke gudana.