Ma'aikaciyar rediyo ta haihu yayin gabatar da shiri

Cassiday Proctor holds her baby, Jameson in hospital Hakkin mallakar hoto @radiocassiday/Instagram
Image caption Cassiday Proctor's baby boy has been named Jameson

Wata mai watsa shirye-shiryen rediyo a Amurka ta haihu yayin da take gabatar da shiri.

Cassiday Proctor, mai gabatar da shirin safe na ranakun aiki na mako a wata tashar da ake kira The Arch a birnin St. Louis na Amurka, ta watsa labarin yadda aka yi mata tiyatar cire jaririnta a ranar Talata.

Ms Proctor ta fara jin nakudar haihuwa ne tun a ranar Litinin. Gidan rediyon da take aiki sun hada kai da asibitin da ta haihu kan yadda za a watsa yadda haihuwar ta kasance a rediyo.

Ta gaya wa BBC cewa ba su shirya zuwan jaririn ba saboda ya zo makonni biyu kafin lokacin da ake tsammanin sa.

Ms Proctor ta ce ta ji dadin iya bayar da labarin daya daga mafi abubuwan da suka fi sa ta farin ciki a rayuwarta ga masu sauraronta a rediyo.

Ta ce "haihuwa a lokacin da take gabatar da shiri tamkar, "kari ne a kan abun da ta saba yi a ko wacce rana a gidan rediyonmu, saboda kullum ina ba da labarin dukkan rayuwata ga masu sauraro."

An sanyawa jaririn suna Jameson, bayan da masu sauraro suka zabi sunan jaririn a cikin wata gasa da aka gabatar a rediyon a watan Janairu.

Labarai masu alaka