BBC ta kaddamar da gasar Komla Dumor ta 2018 ga 'yan jaridar Afirka

Bayanan bidiyo,

Gasar Komla Dumor ta BBC ta 2018

BBC na neman 'yan jaridar Afirka masu tasowa don shiga gasar tunawa da Komla Dumor ta 2018, wadda wannan ne karo na hudu a jere da aka yi gasar.

Ana gayyatar 'yan jarida daga nahiyar Afirka da su shiga gasar, wadda aka kirkire ta da nufin zakulo da kuma taimakawa 'yan jarida masu fasaha daga Afirka.

Wanda ya yi ko ta yi nasara za sushafe wata uku a hedikwatar BBC da ke London, don kara gogewa da sanin makamar aiki.

Za a rufe shiga gasar ranar 23 ga watan Maris na 2018, da misalin karfe 11:59 agogon GMT.

An kikrkiri gasar ce domin tunawa da kuma girmama dan kasar Ghana Komla Dumor, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a tashar labarai ta BBC, wanda ya yi mutuwar farat daya a shekarar 2014, a lokacin yana da shekara 41 a duniya.

A wannan shekarar za a kaddamar da gasar ne a Accra, babban birnin kasar Ghana.

  • Za ku iya latsa nan don samun karin bayani game da gasar da kuma sanin ko kun dace da shiga (Ku latsa nan)

It will be made to an outstanding individual living and working in Africa, who combines strong journalism skills, on-air flair, and an exceptional talent in telling African stories with the ambition and potential to become a star of the future.

Bayan shafe wani lokaci da wanda ya yi nasara zai yi a London, zai/za ta kuma je wata kasa a Afirka don yin labari kan wani abu - za kuma a rarraba labarin ga kasashen Afirka da ma duniya baki daya.

Bayanan hoto,

2017 winner Amina Yuguda reported on environmental issues during her time at the BBC

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wadanda suka yi nasara a baya sun hada da Nancy Kacungira daga Uganda da Didi Akinyelure daga Najeriya da kuma Amina Yuguda ita ma 'yar Najeriya.

A nata aikin, Amina ta je kasar Uganda ne inda ta yi labarin kan: Yadda Tafkin Victoria ke fuskantar barazana, wanda shi ne tafki ma fi girma a Afirka, wanda masana kimiyya suka yi gargadin cewa yana mutuwa.

Amina ta ce: "Samun nasarar da na yi a gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017 ta sa na ji tamkar a lokacin ne na fara aikin jarida. Cin gasar babar kafar yada labarai ta duniya, da samun girmamawa a wajen, sun sa na ji tamkar yanzu ne ma nake jin na fara aikin jarida."

Ta kara da cewa: "A lokacin da na je Landan don kara samun kwarewa, na gane muhimmancin yin labaran gaskiya, da tsage gaskiya, da jin ko wanne bangare da yin adalci yayin rubuta labarai, da kuma sanin yadda zan rubuta labaran da suka shafi Afirka da kyau ta yadda sauran duniya za su fahimta.

"Muna alfahari da yadda Komla ya wakilci nahiyarmu da ma duniya, kuma na ji dadi da na zamo cikin wadanda za su dora daga inda ya tsaya.

Amina za ta kasance cikin wadanda za su kaddamar da gasar ta 2018, tare da daraktan yada labarai na BBC Jamie Angus.

Da yake magana gabanin kaddamarwar ya ce: "Abun alfahari ne kasancewata a Ghana, kasar su Komla, cikin 'yan uwansa da abokansa, don karrama shi, da kuma zakulo wani ko wata sabuwar tauraron 'yan jarida na Afirka.

Mutane ukun da suka taba lashe gasar - Nancy da Didi da Amina - duk sun suna basirarsu ta aikin jarida, da matukar sanin nahiyar Afirka, da kuma sanin yadda za su bai wa masu sauraro labari irin yadda suke so.

"Muna ci gaba da neman 'yan jarida masu kwazo daga nahiyar da kuma yi musu maraba a BBC a matsayin wadanda suka lashe gasar Komla Dumor."