An tilasta wa yara kallon yadda ake yi wa iyayensu fyade a Sudan ta Kudu

Wadansu mata masu zanga-zanga a Sudan ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A watan Disamban da ya wuce ne aka yi zanga-zangar adawa da wahalar da mata da yara suke fuskanta a kasasr

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce ana tilastawa yara a kasar Sudan Ta Kudu kallon yadda ake yi wa iyayensu fyade.

Wani rahoto da masu binciken kare hakkin bil adama na MDD suka fitar, ya ce wasu jami'ai 40 na iya zama wadanda ke da alhakin aiwatar da laifukan yaki da kuma laifukan cin zarafin bil adama.

Rahoton ya ce ana azabtar da fararen hula da cin zarafinsu, kuma an lalata kauyuka da dama.

Ana ci gaba da rikici tsaknain bangarorin gwamnati biyu masu adawa da juna a Sudan ta Kudu, duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanyawa hannu a shekarar 2015.

Daga cikin manyan jami'an 40 da aka samu da hannu a aikta wadannan miyagun laifuka, har da wadansu kanal din soji biyar da kuma gwamnonin jihohi uku.

Sai dai rahoton bai ambaci sunayensu ba, amma za a bayyana hakan idan aka fara shari'ar a nan gaba.

MDD ta ce hujjojin da aka tattara daga wadanda abin ya shafa "suna da ta da hankali" ciki har da yadda wadansu 'yan uwa aka tilasta musu su yi wa danginsu fyade "kamar yadda ya faru a Bosniya."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wata mata ta ce an tilasta wa danta mai shekara 12 ya tara da kakarsa a bakin ransa, kafin daga bisani aka yi wa mijinta dandaka a gabanta.

Shi kuwa wani mutum ya ga yadda aka yi wa dan uwansa fyade ne, kafin daga bisani a jefar da gawarsa a daji.

"Cin zarafin maza ya zama ruwan dare a Sudan ta Kudu," in ji shugabar hukumar da ke kula da kare hakkin dan Adam a Sudan ta Kudu, Yasmin Sook.

"Abin da muke gani yanzu kadan ne daga cikin abin da ke faruwa," a cewarta.

Wata mata mai dauke da juna biyu a yankin Lainya ta ce ta gane wa idonta yadda mayakan SPLA suke azabtarwa da kuma fulle kawunan wadansu da ake zargi magoya bayan 'yan adawa ne.

Kuma an tilasta mata zama a daki guda da gawawwakin mutanen da ke rubewa - guda daga cikinsu kuma gawar mijinta ta ce.

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya suna ci gaba da tattara hujjoji wadanda za su gabatar a kotunan da ke sauraron shari'ar manyan laifukan yaki.

Kuma sakamakon binciken za a gabatar da shi ne a gaban kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva.

Sai dai zuwa yanzu ba a kafa kotun ba saboda majalisar dokokin Sudan ta Kudu ba ta amince da bukatar kan ba tukuna.