Mene ne yake hana mata zuwa awon ciki?

Bayanan sauti

Mene ne yake hana matan karkara zuwa awon ciki?

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin:

Yin awo ga mata masu juna biyu abu ne mai matukar muhimmanci, inda ake duba lafiyarsu da ta jariran da ke cikinsu kafin haihuwa.

A ka'ida kamata ya yi a ce mace ta fara zuwa asibiti don yin awo da zarar ta fahimci tana da juna biyu, don sanin yadda za ta kula da kanta da jaririnta.

Haka kuma a lokacin da take zuwa awon ciki za ta yi wasu alluran rigakafi, da sanin yadda za ta shiryawa haihuwa, da irin yadda za ta samu taimako kan laulayin ciki.

Sai dai abin takaicin shi ne a arewacin Najeriya akwai matsloli da dama da suka baibaye batun zuwa awon ciki da haihuwa a yawancin asibitoci.

Wadannan matsaloli su suke haifar da sanadin da ke sa ana yawan samun mace-macen mata masu ciki yayin haihuwa da ma jariransu.

A asibiti guda kawai, a bisa kiyasi, mata biyar ne ke mutuwa a kullum yayin haihuwa sakamakon matsalolin da za a iya magance su idan ana zuwa awo, kamar yadda wata ma'aikaciyar jinya ta shaida wa Adikon Zamani.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu kafofin yada labarai dai sun ce akalla mata 146 ne ke rasa rayukansu kullum a fadin Najeriya a lokacin da suka zo haihuwa.

A wasu wuraren sam mata ba sa son zuwa asibiti don duba lafiyarsu a yayin da suke da juna biyu, sun gwammace su sha jike-jike da wasu saiwoyi na gargajiya a matsayin abun da zai taimakawa lafiyarsu da ta jariran.

Sai dai matsalar ita ce, duk mai juna biyun da ba ta zuwa asibiti don yin gwaji, to tamkar makaho ne da ke tsallaka titi ba dan jagora. Wannan abu da suke yi kasada ce kuma hadari ne ga lafiyarsu.

Kwararru a fannin lafiya sun sha nanata cewa idan har mace na son haihuwa lafiya kalau ba tare da tangarda ba, to hakika tana bukatar ta dinga zuwa asibiti domin a duba lafiyarta da ta jaririn.

Kuma a asibitin ne za a gane yanayin da jaririn yake ciki a ciki, da lafiyar ita kanta uwar, sannan ana iya gane ko za ta ci karo da wata tangarda kafin lokacin haihuwa ya zo, wanda hakan zai sa a shirya duk wani taimako da za ta bukata a ranar haihuwar.

A wannan makon shirin Adikon Zamani ya bi diddigin dalilin da ya sa mata ba sa son zuwa awon ciki musamman a yankunan karkara, inda muka ganewa idonmu matsaloli daban-daban da mata ke ciki dangane da rashin zuwa awo da kuma wadanda suke cin karo da su a lokacin haihuwa.