Buhari 'yana yi wa 'yan Nigeria romon-baka'

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Buhari 'yana yi wa 'yan Nigeria romon-baka'

Wani fitaccen dan siyasar Jamhuriya ta biyu a Najeriya, Dr Junaidu Muhammad ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana yi wa 'yan kasar romon-baka a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

Dr Muhammad ya shaida wa BBC cewa shugaban kasar da manyan hafsoshin rundunar sojin sun sha yi wa 'yan kasar karya kan hakikanin halin da ake ciki a yakin, shi ya sa bai yi mamakin sace 'yan makarantar sakandare ta Dapchi da ke jihar Yobe ba.

"Satar yaran da aka yi ta ba da tabbataccen yakinin cewa babu tsaro a kasar nan; ya nuna cewa abubuwan da ke fitowa daga shugaban kasa da fadarsa romon-baka ne, ba gaskiya ba," in ji dan siyasar.

Dan siyasar ya kara da cewa ce nade-naden da Shugaba Buhari ya yi a rundunonin sojin kasar ya yi su ne bisa son rai ba cancanta ba.

A cewarsa, mafita ga halin da kasar ke ciki ita ce Shugaban kasa ya sallami dukkan hafsan hafsoshin tsaron kasar "idan ba haka ba babu abin da zai sauya."

Labarai masu alaka