Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da 'yan Afirka a makon jiya.

Kenya Wildlife Service lift a tranquillized elephant bull into an truck at the Lamuria, Nyeri county, on February 21, 2018 during the transfer of elephants from Solio, Sangare and Lewa to northern part of Tsavo East National Park in Ithumba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ba ko yaushe ne ake ganin giwa a rigingine kuma a sama ba - amma abin da ya faru kenan ranar Laraba a lardin Nyeri na kasar Kenya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A can birnin Abidjan da ke Ivory Coast, mutane ne ke tashi sama lokacin bikin Circus karon farko.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A Zimbabwe, mutane ne suka taru domin yin alhinin mutuwar jagoran jam'iyyar Movement for Democratic Change (MDC) Morgan Tsvangirai, wanda ya mutu yana da shekara 65.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar ne kuma wata mata ta haifi sambacecen jaririnta a wani asibitin da ke Juba, babban birnin Sudan ta Kudu. Kasar na cikin kasashen da suka fi hatsari a rayu a cikinsu, in ji hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya, Unicef, a wani sabon rahoto da ta fitar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A Habasha, tsofaffin sojoji sun yi alhinin tunawa da kisan kare-dangin da aka yi a Addis Ababa, inda sojojin mamaye na Italiya suka kashe akalla 'yan kasar 20,000 ranar 19 ga watan Fabrairun 1937.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Su ma 'yan kasar Libya sun yi bikin tunawa da wata muhimmiyar rana a makon jiya. 17 ga watan Fabrairu ce ranar da aka cika shekara bakwai da tumbuke gwamnatin Kanar Muammar Gaddafi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A can Masar kuwa, shirye-shirye ake yi na gudanar da zabe. Magoya baya sun kafa kyallayen yakin neman zabe a birnin Alkahira, cikin har da na yakin neman zaben Shugaba mai-ci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ba a yi zabe a Afirka ta Kudu ba, amma an nada sabon shugaban kasa. Wannan hoton Cyril Ramaphosa ne kafin ya yi jawabi ga 'yan kasar. Za mu so sanin abin da wannan matar da ke kusa da shi ta hango.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A Korea ta Kudu, wannan dan kasar ta Ghana dan wasan Sululun tafi-da-ká, Akwasi Frimpong, ya shiga filin wasa dauke da 'yarsa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A Kenya, an mayar da hankali ne kan gasar da ke tafe - wato gasar cin kofin kasashen kungiyar Commonwealthda za a yi a Australia a watan Afrilu.

Images courtesy of AFP and EPA