An kashe wasu mahara a cocin Afirka ta Kudu

An kama mutum goma da ake zargi da hannu a harin sannan wasu kuma sun tsere.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kama mutum goma da ake zargi da hannu a harin sannan wasu kuma sun tsere.

Jami'ai a Afirka ta Kudu sun ce 'yan sandan kasar sun harbe har lahira mahara bakwai a ba-ta-kashin da suka yi a wani cocin da ke Eastern Cape.

Sun ce maharan da aka kashe sun buya ne a cikin cocin bayan sun kai hari kan wani ofishin 'yan sanda ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 'yan sanda biyar da wani soja.

An kama mutum goma da ake zargi da hannu a harin sannan wasu kuma sun tsere.

Hukumomi sun ce har yanzu ba a san dalilin da ya sa maharan suka kai farmakin ba, ko da yake sun saci makamai a lokacin da suka kai harin.

Ana kashe jami'an tsaro da dama a duk shekara a Afirka ta Kudu, sai dai harin da aka kairanar ta Laraba ya janyo tofin Alla-tsine kuma shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya yi kira da a kama maharan sannan a yi bayani kan batun.